Kafa ‘yan sandan jihohi zai mayar da Nijeriya baya – CP ‘Singham’

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda, Muhammad Wakili, wanda aka fi sani da CP Singham, ya bayyana rashin goyon bayansa ga shirin kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa matakin zai iya mayar da Nijeriya ga irin matsalolin da suka sa aka soke tsarin a shekarar 1972.

A wata hira da ya yi da NewsBreakNaija, Wakili ya ce Nijeriya ta taba gwada tsarin ‘yan sandan jihohi a baya, amma an samu kalubale da suka hada da amfani da rundunar wajen cimma manufofin siyasa.

Ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai magance matsalolin tsaro da ake fama da su a yanzu, yana mai jaddada cewa matsalar Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ba tsarin gudanarwa ba ne, illa rashin isassun jami’ai, karancin kudade, rashin kayan aiki da kuma rashin ingantaccen horo.

A cewarsa, idan aka samar wa rundunar kayan aiki na zamani tare da daukar karin jami’ai da inganta walwalarsu, za ta iya gudanar da aikinta yadda ya kamata.

Dangane da batun yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kungiyar Boko Haram, Wakili ya ce ba ya ganin ‘yan sandan jihohi za su fi Rundunar ‘Yan Sandan Tarayya iya magance wadannan matsaloli.

Ya kuma yi gargadin cewa gwamnoni na iya amfani da rundunar ‘yan sandan jihohi wajen cimma muradun siyasa, musamman a lokutan zabe, yana mai cewa hakan zai iya kawo barazana ga dimokuradiyya da adalci.

Sai dai ya bayyana cewa idan har za a kafa ‘yan sandan jihohi, dole ne dokar da za ta kafa rundunar ta fayyace aikinta, iyakokin ikonta, tsarin gudanarwa da kuma hanyoyin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Wakili ya kuma bukaci gwamnati da ta ba masana da sauran masu ruwa da tsaki damar bayar da gudunmawa wajen tsara dokar kafa ‘yan sandan jihohi, domin tabbatar da cewa an yi la’akari da duk wani kalubale da ka iya tasowa.

Ya kara da cewa mafita ga matsalolin tsaron Nijeriya ita ce tabbatar da adalci, gaskiya, kishin kasa, tsoron Allah da kuma inganta Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya maimakon kafa wata sabuwar runduna.

By ukarofi

Leave a Reply