Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jingine hukuncin kotun Oyo na barin ɗalibai mata sanya hijabi a UI International School

Spread the love

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Ibadan ta jingine hukuncin Babbar Kotun Jihar Oyo da ya ba ɗalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a makarantar International School da ke ƙarƙashin Jami’ar Ibadan.

A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta bayyana cewa makarantar makaranta ce mai zaman kanta, don haka tana da ikon tsara dokokinta na tufafi da tsarin ɗabi’a ba tare da katsalandan ba.

Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da wasu iyaye Musulmai suka shigar suna neman a ba ’ya’yansu damar sanya hijabi a makarantar, suna mai cewa hakan wani ɓangare ne na ’yancin addininsu.

Tun farko, babbar kotun Oyo ta amince da buƙatar, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin iyaye, malamai da ƙungiyoyin addini.

Sai dai kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukuncin farko bai yi la’akari da matsayin makarantar a matsayin mai zaman kanta ba, don haka ta soke shi tare da dawo da dokar hana sanya hijabi a makarantar.

Hukuncin ya sake tayar da kura kan batun ’yancin addini da dokokin makarantu a Nijeriya, inda mutane da dama ke cigaba da bayyana ra’ayoyinsu akan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply