04
Jul
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Ibadan ta jingine hukuncin Babbar Kotun Jihar Oyo da ya ba ɗalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a makarantar International School da ke ƙarƙashin Jami'ar Ibadan. A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta bayyana cewa makarantar makaranta ce mai zaman kanta, don haka tana da ikon tsara dokokinta na tufafi da tsarin ɗabi’a ba tare da katsalandan ba. Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da wasu iyaye Musulmai suka shigar suna neman a ba ’ya’yansu damar sanya hijabi a makarantar, suna mai cewa hakan wani ɓangare ne na ’yancin addininsu. Tun farko, babbar kotun…
