Babaji

4782 Posts

Kotu ta tabbatar da shugabancin David Mark a ADC

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta tabbatar da halaccin shugabancin tsagin su Sanata David Mark a jam'iyyar ADC da kuma yin watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide ta ƙalubalantar naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar na ƙasa. Mai shari'a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam'iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam'iyyar ba kafin ya garzaya kotu. Kotun ta kuma yanke cewa miƙa shugabancin…
Read More

Kofin Duniya: Ingila za ta kara da Mexico a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya na 2026, ƙasashen Ingila da Mexico sun haye zuwa zagayen 'yan 16 bayan nasarorin da suka samu a wasannin 'yan 32. Ingila ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen 'yan 16n ne bayan doke Jamhuriyar Kongo da ci 2 da 1 a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka. Da fari, Kongo ce ta samu damar jan ragamar wasan bayan zura ƙwallo guda ta hannun Brian Cipenga a minti na bakwai da fara wasan. Daga bisani Harry Kane ya farke ana sauran minti…
Read More

Ingila ta kai zagayen ‘yan 16 bayan doke Kongo yayin da Kane ya zura ƙwallo biyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba ƙasar Ingila ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen 'yan 16 bayan doke Jamhuriyar Kongo da ci 2 da 1 a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka. Da fari, Kongo ce ta samu damar jan ragamar wasan bayan zura ƙwallo guda ta hannun Brian Cipenga a minti na bakwai da fara wasan. Daga bisani Harry Kane ya farke ana sauran minti 15 a kammala wasan, sannan ya kuma ƙara a minti na 86 duk ta hannun sabon ɗan wasan Barcelona Anthony Gordon, lamarin da ya ba Three Lions damar…
Read More

‘Yan bindiga sun buƙaci fansa yayin sace lauya bayan taron MULAN a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani masanin harkar shari'a mai suna Hashim Abdullahi ya shiga hannun 'yan bindiga yayin da yake koma wa gida daga taron ƙasa na Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi ta Ƙasa (MULAN) da aka gudanar a Jihar Kano. Tsohon shugaban MULAN, Sa'idu Muhammad Tudun-Wada ne ya tabbatar da batun a wata sanarwa da jaridar NigerianSketch ta samo a ranar Laraba. A cewar sanarwar, an yi garkuwa da Abdullahi ne a lokacin da yake kan hanyar koma wa garin da yake zama a Jihar Kebbi bayan halatar taron. Sa'idu Tudun-Wada ya bayyana cewa, masu garkuwar sun tattauna da…
Read More

DSS ta miƙa wa ICPC tsohon Minista, Uche Nnaji bayan kama shi a filin jiragen saman Abuja

An kama tsohon Ministan Ƙirkire-ƙirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a filin jirgin saman Akanu Ibiam International Airport da ke Enugu, yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Abuja a safiyar ranar Laraba. Rahoton Premium Times ya ce an tsare Nnaji ne domin miƙa shi ga hukumar Yaƙi da Cin-Hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka ICPC domin ci gaba da bincike kan zargin ƙirƙirar jabun takardun karatu. Ana zargin wannan batu ne ya sa ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Oktoban shekarar 2025. Kamen nasa ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya…
Read More

Shugaban Optimal Image Media ya jinina wa Gwamnan Kebbi kan magance matsalolin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Kamfanin Optimal Image Media Limited da gidan talabijin na 3rd Eye Africa, Alhaji Shuaibu Mungadi, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro da kuma aiwatar da ayyukan ci-gaba a sassan jihar. Mungadi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da tawagar yaɗa labaran gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu, Alhaji Yakubu Ahmed BK ta kai masa ziyarar wayar da kai a ofishinsa da ke Abuja. Ya bayyana cewa, ayyukan gwamnan sun cancanci yabo, waɗanda daga cikinsu akwai…
Read More

Norway za ta kara da Brazil bayan doke Ivory Coast a zagayen ‘yan 32

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Norway ta tsallake zuwa zagayen 'yan 16 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka, bayan doke Cote d'Ivoire da ci 2 da 1 a zagayen 'yan 32. Wannan shi ne karo ne farko da Norway take samun nasara a irin zagayen bayan sau uku tana yunƙuri, kamar yadda ita ma Ivory ta rasa nasara a wasan farko cikin guda bakwai da ta buga a baya. A minti na 39 ne ɗan wasa Antonio Nusa ya zura ƙwallo a ragar mai tsaron gida Yahia Fofana, wanda ya ba Norway…
Read More

Babban basarake a Kwara ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani Sarkin gargajiya kuma Obajisun na Masarautar Ayedun da ke Jihar Kwara mai suna Oba Dakta Olusegun Abayomi JP ya rasu a ranar Talata. Abayomi ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Afr Babalola da ke Ado Ekiti a Jihar Ekiti bayan fama da wani gajeren rashin lafiya. Marigayin, wanda ya yi bikin cika shekaru 85 a ranar 16 ga Mayu, 2026 ya shahara da nagartar jagoranci tun daga tushe kuma wanda ya samar da sauye-sauyen ci-gaba ga Masarautar Ayedun. Haka kuma yana ɗaya daga cikin sarakuna 10 da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq…
Read More

Kotun Ƙolin Amurka ta ƙi amince wa buƙatar Trump ta taƙaice ‘yancin zama ɗan ƙasa ta haihuwa

A ranar Talata Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da buƙatar Shugaba Donald Trump na ƙasar ta yunƙurin neman a taƙaice bayar da shaidar zama ɗan ta hanyar haifar mutum a ƙasar, hukuncin da ya jaddada 'yancin zama ɗan ƙasa ga duk wanda aka haifa a Amurka. A cewar Kotun, duk wanda aka haifa a Amurka na da damar mallakar shaidar zama ɗan ƙasa. A shekarar da ta gabata ne Trump ya rattaɓa hannu akan wata doka da ke neman haramta wa yaran da aka haifa a ƙasar waɗanda iyayensu ke zama a Washington ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma…
Read More

Rikicin ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu ya tilasta wa ‘yan Nijeriya da wasu tserewa

An fara zanga‑zangar ƙyamar baƙi a sassa daban‑daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa aka jibge jami’an tsaro saboda fargabar rikice‑rikice. Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga‑zangar su guji tashin hankali, yana mai jaddada cewa dole ne a gudanar da zanga‑zanga cikin lumana ba tare da tsoratarwa ba. Zanga‑zangar na da alaƙa da wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takardu su fice daga ƙasar. Hakan ya sa mutane da dama suka fara tserewa saboda tsoron hare‑hare, yayin da hukumomi suka ce an riga an mayar da sama da mutum 25,000 kasashensu,…
Read More