10
Jun
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano ta fitar da takardar hana kama ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar NNPP a babban zaɓen shekarar 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai, wacce ke ƙunshe da hana kamawa ko cin mutunci ko kuma tsare su. Mutanen sun haɗa da Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Clement Anele, Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Mai Shari'a Yusuf Ubale Muhammad ya fitar da takardar dake ɗauke da bayanin wanda ya fara aiki daga ranar 5 ga watan yunin shekararnan. Kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar…
