30
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta umarci a yi wa tsarin ilimin Nijeriya garambawul, sakamakon rahoton da ke nuna cewa kusan ɗalibai miliyan 20 sun fice daga makaranta. Ministan Ilimin, Dakta Tunji Alausa ne ya sanar da haka yayin ƙaddamar da Kwamitin Ministoci na Aiwatarwa da Sanya ido na Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC) a Abuja. Ya ce, tsarin raba raba makarantar sakandare ƙarama, wato Junior Secondary School (JSS) da Senior Secondary School (SSS) ya gaza samar da mafita ga yawan ɗaliban da ba sa zuwa makaranta. A madadin haka, ya ce za a samar da wani tsari…
