29
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabas, sun yi nasarar kama wani da ake zargin ɗan tsegumi ne ga ƙungiyar ISWAP bisa zargin wani shiri na kai farmaki ga sansanin sojoji guda biyu a Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Shuaibu ne sunan wanda ake zargin, wanda dakarun Bataliya ta 212 da ke sansanin ayyuka (FOB) na yankin Chabbol suoa yi ram da shi bayan samun wani bayanin sirri akan shirin ƙaddamar da farmakin. Wata majiyar sojoji ta shaida wa manema labarai cewa, an kama Shuaibu ne yayin wani sintiri…
