Babaji

4782 Posts

Mashigar Hormuz: Amurka ta yi ruwan wuta a Iran

Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan wani jirgin sama mara matuki ya kai hari kan wani babban jirgin ɗaukar kaya a Mashigin ruwan Hormuz. Harin ya faru ne kusa da gabar tekun Oman, inda aka kai wa jirgin ruwan Ever Lovely mai tutar Singapore hari. Jirgin mallakar kamfanin jigilar kaya na Taiwan, Evergreen Marine, ne. Babu wani ma’aikacin jirgin da ya ji rauni, kuma jirgin ya samu damar ci gaba da tafiyarsa. Rundunar sojin Amurka ta ce ta dakile wasu jirage marasa matuka da ake zargin suna cikin harin. Trump ya bayyana…
Read More

DSS ta sako manomin da aka danganta da Boko Haram bisa kure, ta biya shi diyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, ta umarci a gaggauta sakin Nura Idris, wato manomin da aka yi kuskuren kamawa bisa zargin hannun a ayyukan ta'addanci, bayan nazari da binciken da aka gudanar akansa sun nuna cewa shi wankakke ne daga hakan. Daraktan Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi ne ya amince da sakin Idris bayan karɓar rahoton ababen da aka gano daga binciken da aka gudanar akansa, wanda a ciki babu wata hujja da ke alaƙanta shi da 'yan ta'addar Boko Haram. Haka kuma, Shugaban na DSS ya umarci a ba Idris Naira miliyan…
Read More

Jihohin Kano, Katsina, Jigawa da wasunsu za su fuskanci duhu yayin da hukumar TCN za ta yi aikin inganta lantarki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa mazauna a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da Yobe za su fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na wani ɗan lokaci a ranar Lahadi sakamakon aikin gyaran cibiyar rarraba wutar lantarki ta Kumbotso da Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ke yi. A cewar rahotannin, an shirya aikin gyaran ne da nufin inganta tsarin samar da wutar lantarki a sassan jihohin. Sannan, za a gudanar da aikin ne domin ƙarfafa tsarin isar da wutar lantarki da inganta hanyoyin samar da wuta a yankunan da abin ya shafa nan gaba. Haka kuma,…
Read More

Ka dakatar da kafa ‘yan sandan jihohi sai bayan zaɓen 2027 – Obi ga Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da aiwatar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi har sai bayan babban zaɓen shekarar 2027. Obi ya bayyana haka ne bayan majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da ƙudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin inganta tsaro da rage nauyin rundunar ‘yan sandan ƙasa. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce duk da cewa kafa ‘yan sandan jihohi mataki ne mai kyau, akwai fargabar cewa tsarin na iya zama abin amfani na siyasa idan aka fara…
Read More

Ba mu samu hukuncin kotu na soke rajistar NDC ba – INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi ainihin kwafin hukuncin Kotun Tarayya da ke Lokoja wanda ya soke umarnin rajistar jam’iyyar NDC ba da aka yi a kwanan nan. Kakakin shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya ce hukumar ta samu rahotannin hukuncin da aka yanke a ranar 26 ga Yuni, 2026, amma ba za ta iya yin cikakken bayani kan hukuncin ba sai bayan ta samu kwafin hukuncin. A cewarsa, sashen shari’a na INEC zai nazarci hukuncin da zarar an karɓi kwafin sannan hukumar ta yanke matakin da ya dace bisa doka. A ranar Juma’a…
Read More

Tinubu ya naɗa Sa’ad Namdas a matsayin daraktan BCDA, Obahiaghon da Umeoji a manyan muƙaman NDPHC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Mia magana da yawun Majalisar Wakilai, Abdulrazak Sa'ad Namdas a matsayin sabon darakta janar na Hukumar Raya Yankunan Iyakokin Nijeriya (BCDA). Wannan na nufin Dakta Namdas ya maye gurbin Dakta Dakorinama Alabo George, wanda ya yi murabus domin neman wani muƙamin siyasa a jiharsa. Namdas tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne da ya wakilci mazaɓar Ganye/Jada/Mayo Belwa/Toungo ta Jihar Adamawa, sannan ya yi takarar neman tikitin gwamna a zaɓen fidda gwani da aka kammala kwanan nan a jihar. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida kuma masani a harkokin…
Read More

Trump ya yi iƙirarin an daina kisan Kiristoci a Nijeriya bayan hare-haren Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun taimaka wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya. Trump ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a birnin Washington ranar Juma’a, inda ya ce matakan da Amurka ta ɗauka a Nijeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen daƙile hare-haren da ake zargin ana kai wa mabiya addinin Kirista a yankunan da ke fama da ta’addanci. Ya bayyana cewa, gabanin matakin, dubban mutane da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi sun rasa rayukansu a hare-haren da…
Read More

Rundunar sojoji ta yi wa manyan jami’anta garambawul, ta naɗa sabbin kwamandoji

Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da sauya muƙaman manyan dakarun rundunar a sassa daban-daban na ayyuka, jagoranci, horaswa da gudanarwa. Rundunar ta ce, matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta aikin sojoji, ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma bunƙasa shirin tunkarar sabbin barazanar tsaro da ke addabar sassan ƙasar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama'a ta riƙo ta rundunar, Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Asabar. Sabbin naɗe-naɗen sun haɗa da nada Manjo Janar WM Dangana a matsayin kwamandan Runduna ta 3 da kuma kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation…
Read More

Nijeriya ta kama sanannun ‘yan ta’adda bakwai suna dawowa daga aikin Hajji a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A makon da ya gabata ne hukumomin tsaro suka kama wasu mutane bakwai da ake zargin sanannun kwamandojin mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa gida Nijeriya daga aikin Hajji. An yi nasarar haka ne a filin jiragen sama na Umaru Musa Yar’Aduada ke Jihar Katsina, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana a ranar Juma'a. Tunji-Ojo, ya bayyana cewa tsarin tantance bayanan ’yan ƙasa na Hukumar NIMC ya taimaka wajen cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka mutum 17 a sabon harin Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a ƙauyen Ruwan Bore na Ƙaramar Hukumar Talata Mafara sun shiga firgici da jimami bayan wani mummunan harin 'yan ta'adda da ya yi ajalin mutane 17 a ranar Juma'a. Bayan harin, Shugaban ƙaramar hukumar, Yahaya Yari ya caccaki Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle bisa rashin cika alƙawuran da ya yi wa sojoji a jihar. Wannan al'amarin ya haifar da damuwa akan rashin tsaro a Jihar Zamfara, inda mazauna suka fito zanga-zanga tare da nuna adawarsu akan ƙamarin rashin tsaron wajen tare babban titin Sakkwato zuwa Gusau na tsawon sa'o'i. Da yake jawabi…
Read More