27
Jun
Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙarar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke na soke umarnin da ya tilasta wa INEC yin rajistar jam’iyyar. A cewarta, ba a soke rajistarta ba, kuma dukkan ayyukanta za su ci gaba kamar yadda aka saba. Hukuncin da Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke ya soke hukuncin da kotun ta bayar a watan Disambar 2025, bayan wata ƙungiya mai suna Peace Movement Party ta yi iƙirarin cewa tambarin da aka yi amfani da shi wajen rajistar NDC nata ne. Shugaban NDC na ƙasa, Moses Cleopas, ya ce jam’iyyar…
