
Kwamitin Wayar da Kan Al’umma game da mahimmancin Katin Zaɓe, a ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar Kano, ya yi gangamin taro na masu ruwa da tsaki kan al’amuran jama’a, tare da haɗakar Ƙungiyoyin Aikin Gayya na ƙananan hukumomi 8 a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Bichi.
Ƙananan hukumomin sune Ɓagwai, Bichi, Dawakin Tofa, Ghari, Rimin Gado, Shanono, da kuma Tsanyawa.
Shugaban Majalisar ƙaramar hukumar da ya karɓi baƙuncin wannan tawaga, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya ja hankalin al’umma da su mayar da hankali wajen fitowa yin rijistar katin zaɓen ga waɗanda ba su samu ikon yi ba, bisa la’akari da wannan karon shi ne na ƙarshe da za a kammala aikin a ranar 10 ga wata mai zuwa na Yuli.
Alhaji Hamza Maifata, ya sake jaddada ƙudirin ƙaramar hukumar na ganin an cimma nasarar wannan aiki bisa yadda suke tsaye tsayin daka na ganin kowane mai haƙƙi a yankin ya mallaki katinsa na zaɓe, sakamakon jajircewa, tare da ɗimbun gudunmawar da jagororin yankin suke bai wa wannan ɓangare, musamman Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar tare da Sanata Barau I Jibrin.
“Duk irin yanayin da kake ciki wannan katin zaɓen zai taimaka maka wajen ko ka fita ko ka shiga, domin abin da kake ganin bai maka ba, za kai amfanin da wannan katin ka zaɓe shi ko ka cire shi.” Alhaji Hamza Sule Maifata.
Da yake jawabi, a kan mahimmancin katin zaɓe daya daga cikin ‘yan kwamitin, Malam Usman Bello, ya fayyace gundarin aikin rijistar a matakai uku da ya zama tilas mutane su fahimta domin kauda tangarɗar dakan iya hana kaɗa ƙuri’a ga mutum kacokan.
Waɗanda ba su taɓa yi ba da waɗanda suka kai shekaru 18 a yanzu, sabuwa za a yi musu, sai kuma batun gyara ga waɗanda tasu ta ɓata ko ta lalace ko ta ƙone, da kuma masu sauya akwatin zaɓe sakamakon sauyin wajen zama, su ma suna da haƙƙin zuwa a sabunta musu rijistar zaɓen, inda ya roƙi al’umma da su taimaka wajen rage aikin rijistar zaɓen da ake fara yi a yanar gizo-gizo a wayoyinsu, ta yadda idan sun je hukumar zaɓe hoto da dangwala yatsa kawai ya rage a yi musu bisa sauƙaƙawa duba da ƙuracewar lokaci.
“Almuhimmu shi ne; kamar yadda katin ɗanƙasa a yanzu ya zama duk abin da za ka yi ko aikin hajji za ka yi sai ka haɗa da shi, to watarana katin zaɓen nan akwai yuwuwar shi ma ya zama haka, musamman ɗanka zai je makaranta kuma ana ba da sikolashif, to wataƙila za a tambaye ka ina katin zaɓenka?” Malam Usman Bello.
A ɓangaren Kwamishinan Ƙananan Hukumomi kuma Shugaban Kwamitin Ƙananan Hukumomi a Kan Karɓar Katin Zaɓe, Alhaji Tajo Muhammad Othman, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Gwmna na Musamman a Kan Wayar da Kan Al’umma tun daga Tushe, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya, ya ce, ziyarar kwamitin a ƙananan hukumomin umarni ne na Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ya kuma ayyana Ƙaramar Hukumar Bichi ta fi dukkan sauran ƙananan hukumomi yawan al’umma da suka mallaki katin zaɓe a hannayensu a bisa alƙaluman jama’ar da suka yi rijistar katin zaɓe na kowace ƙaramar hukuma, sakamakon haka ya ja hankalin ɗaukacin al’ummar jihar Kano dangane da jaddada mahimmancin katin zaɓe ga kowane ɗankasa.
“Yanzu wannan ƙuri’ar zaɓen kusan ita ce a madadin ƙidaya ta sensus, wannan botas kad ɗin da ake cewa mu yi ta shafi tattalin arzikinmu da ilimunmu da nomanmu da tsaronmu tare da duk wani abin da ba ma tsammani.” Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya.
Ƙarshe daga cikin mahalarta taron da yawa sun bayar da muhimman shawarwari da kwamitin ya gamsu da su ɗari bisa ɗari, da suka haɗa da: Daraktan Mulki na yankin, Alhaji Abba Muhammad Ɗiso, HOD Kwamuniti Shanno, Kansilan Kwamuniti D/Tofa, Jami’in Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Ƙasa na Shanono, Mataimakin Shugaban Aikin Gayya na jihar Kano, mamba na Ƙungiyar Masu Buƙata ta musamman da kuma Malama Na’ima Yahya Sa’id daga Hukumar Raya Karkara da Birane ta Kano
Taron ya samu halartar Shugaban Ƙaramar Hukumar Tsanyawa, Alhaji Abdullahi Ishaq ‘Yan’awaki tare da wakilcin sauran shugabannin waɗannan ƙananan hukumomi takwas da daraktoci da HODs da masu ruwa da tsaki kan harkokin mutane da ƙungiyoyin jama’a daban-daban da suka kunshi mata da maza; manya da matasa da kuma sauran al’umma.






