
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A makon da ya gabata ne hukumomin tsaro suka kama wasu mutane bakwai da ake zargin sanannun kwamandojin mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa gida Nijeriya daga aikin Hajji.
An yi nasarar haka ne a filin jiragen sama na Umaru Musa Yar’Aduada ke Jihar Katsina, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana a ranar Juma’a.
Tunji-Ojo, ya bayyana cewa tsarin tantance bayanan ’yan ƙasa na Hukumar NIMC ya taimaka wajen cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajjin 2026.
A cewarsa, an kama mutanen ne a Alhamis bayan sun dawo daga Makka, sannan aka miƙa su ga Hukumar Tsaro ta DSS domin ci gaba da bincike.
Ya ce an samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne saboda haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya tare da alaƙarsu da tsarin bayanan Interpol.
Ya bayyana cewa sabuwar dokar NIMC za ta ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar haɗa bayanan hukumomi daban-daban, tare da taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanai da sauran laifukan tsaro.
Ministan ya ƙara da cewa a baya tsarin bayanan ’yan ƙasa a Najeriya ya kasance a rarrabe, amma yanzu ba za a iya samun fasfo na Najeriya ba tare da amfani da bayanan NIMC ba.
Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar NIMC ta 2026 a gaban shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu manyan jami’an gwamnat, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
