Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayyar Nijeriya ta kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da ya haɗa da jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da kuma Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, domin nemo mafita ga matsalar ɓoye iskar gas na girki (LPG) da kuma karkatar da shi zuwa ƙasashen maƙwabta.
Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) ce ta ce, an shirya taron ne bayan hauhawar farashin gas ɗin girki da aka samu a baya-bayan nan, tare da manufar samar da hanyoyin haɗin gwiwa da za su inganta wadatar kayayyakin, sauƙaƙa farashinsu da kuma tabbatar da daidaiton kasuwa a faɗin ƙasar.
Hukumar ta bayyana cewa taron ya haɗa manyan jami’an gwamnati, masu tsara dokoki, kamfanonin samar da gas, ’yan kasuwa, masu gudanar da tashoshin ajiya da kuma ƙungiyoyin masana’antu domin nazarin musabbabin tashin farashin LPG da kuma amincewa da matakan da za su ƙarfafa sarkar samar da kayayyakin.
Yayin da take jawabi a wajen taron, Sakatariyar Dindindin ta Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Patience Oyekunle, ta bayyana LPG a matsayin muhimmin makamashi da gidaje ke amfani da shi, tare da cewa yana daga cikin ginshiƙan manufofin Nijeriya na sauya tsarin makamashi.
Ta ce, tashin farashin gas na ƙara wa iyalai nauyi wajen gudanar da rayuwa tare da haɓaka farashin kayayyaki da ayyuka, saboda haka akwai buƙatar haɗin kai domin tabbatar da samun gas mai sauƙin farashi.
Shi ma ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da harkokin Gas, Ekperikpe Ekpo, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa matuƙa kan tasirin da hauhawar farashin gas ke yi wa ’yan Nijeriya, kuma ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar.
Ya jaddada cewa ƙara yawan samar da gas kaɗai ba zai wadatar ba sai an inganta hanyoyin sufuri, kayayyakin more rayuwa da kuma tsarin farashi mai gaskiya domin al’umma su amfana da duk wani gyara da ake yi a fannin.
A nasa jawabin, Babban Jami’in Gudanarwa na NMDPRA, Malam Rabiu Umar, ya bayyana cewa tsadar shigo da LPG na ci gaba da taka rawa wajen hauhawar farashinsa, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa matakan da ake ɗauka a halin yanzu za su fara rage matsin lamba a kasuwa nan ba da jimawa ba.
Ya ƙara da cewa, hukumar na aiki tare da masu samar da kayayyaki da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara yawan gas da ake samarwa a cikin gida, ƙarfafa sa ido kan kasuwa da kuma tabbatar da wadatar kayayyakin ga masu amfani.
A cikin wani bayani da Daraktan Sashen Tsarin Rarrabawa, Ajiya da Kayayyakin More Rayuwa na Kasuwancin Mai (DSSRI), Ogbugo Ukoha, ya gabatar, NMDPRA ta bayyana gibin kayayyakin more rayuwa, ƙarancin samar da gas a cikin gida, matsalolin jigilar kaya, karkacewar kasuwa da kuma matsalolin samar da kayayyaki a duniya a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa tashin farashin LPG.
Sai dai ya ce an samu ci gaba bayan tattaunawar da aka yi da masu samar da kayayyaki da masu gudanar da tashoshin ajiya. A cewarsa, adadin kwanakin da iskar gas ke iya wadatar da ƙasa ya ƙaru daga kwanaki 11 zuwa kwanaki 22, yayin da matsakaicin yawan gas da ake samarwa a kullum ya tashi daga metric ton 4,262 a watan Mayun 2026 zuwa metric ton 5,040 a watan Yunin 2026.
Masu ruwa da tsaki a sarkar kasuwancin LPG sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin gwamnati, yayin da suka yi nuni da ƙalubalen da ke tattare da ajiya, sufuri, rarrabawa da ingancin kasuwa baki ɗaya.
Daga cikin matakan da aka amince da su akwai ƙarfafa sa ido kan kasuwa, tsaurara hukunci kan masu aikata ba daidai ba, faɗaɗa cibiyoyin ajiya da rarrabawa, ƙara samar da gas a cikin gida, inganta hanyoyin bibiyar kayayyaki, samar da sahihan bayanan kasuwa da kuma zurfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
A jawabin rufe taron, Ministan ya umarci dukkan masu ruwa da tsaki da su fara ɗaukar matakan gaggawa domin ƙara wadatar gas, kawar da matsalolin da ke hana ingantaccen aiki da kuma kare muradun masu amfani da kayayyakin.
Ya ce za a auna nasarar waɗannan matakai ne ta hanyar ƙaruwa a wadatar LPG, inganta tsarin rarrabawa da kuma rage matsin farashi a faɗin Nijeriya.
