Hukumomin NASENI da REA sun ƙulla yarjejeniyar ƙera na’urorin solar na gida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya na ci gaba da yunƙurin rage dogaro da kayayyakin makamashin hasken rana da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, bayan Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani wajen samar da wata muhimmiyar yarjejeniya tsakanin Hukumar Kula da Bincike da Bunƙasa Injiniyanci ta ƙasa (NASENI) da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA) domin fara ƙera kayayyakin solar a cikin ƙasa.

An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ne a Abuja a ranar Litinin, inda aka amince da haɗin gwiwar da zai ƙara haɓaka samar da na’urorin hasken rana, batir, inverter da sauran muhimman kayan aikin makamashi a cikin gida.

Rahotanni sun nuna cewa wannan yarjejeniya na daga cikin shirin rage dogaro da shigo da kayayyakin makamashi da ake ƙiyasta kuɗinsu ya kai dala biliyan 400 a duk shekara. Ana sa ran shirin zai samar da guraben ayyukan yi tare da rage tsadar wutar lantarki ga miliyoyin ’yan Nijeriya.

Shugaban Hukumar Kula da Sayen Kaya ta Gwamnati (BPP), Dakta Adebowale Adedokun, wanda ya jagoranci kulawa da rattaba hannun yarjejeniyar, ya bayyana cewa wannan mataki na cikin aiwatar da manufar “Nijeriya A Farko” da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.

Ya ce sabon tsarin sayen kayayyaki na gwamnati zai ba da fifiko ga masana’antun cikin gida a fannin makamashi.

A cewarsa, “Wannan aiki ne, ba magana ba. Umarnin Shugaban Ƙasa a bayyane yake: dole mu gina ƙarfin cikin gida, mu kare ayyukan ’yan Nijeriya, kuma mu tabbatar da cewa duk kuɗin gwamnati yana haifar da ainihin ci gaban more rayuwa.”

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Hukumar NASENI za ta yi amfani da ƙwarewarta a fannin bincike da injiniya wajen ƙira tare da gwada kayayyakin makamashin hasken rana, yayin da REA za ta shigar da kayayyakin da aka ƙera a Nijeriya cikin ayyukan samar da wuta a ƙasa baki ɗaya, musamman a yankunan karkara da tsarin mini-grid.

Babban Darakta-Janar na REA, Abba Abubakar Aliyu, ya ce haɗin gwiwar zai rage manyan matsalolin da ke hana ci gaban makamashin sabuntawa a Nijeriya, musamman tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma jinkirin aiwatar da ayyuka.

Ya ce, “Shekaru da dama muna fitar da biliyoyin daloli wajen sayen abin da za mu iya kera a nan gida. Wannan yarjejeniya ta kawo sauyi. ƙera kayayyaki a cikin gida zai rage farashi, zai hanzarta ayyuka, kuma zai samar da dubban ayyukan yi ga matasa da injiniyoyi.”

Masana harkokin makamashi sun bayyana cewa Najeriya na shigo da sama da kashi 80 na kayayyakin hasken rana duk da cewa tana da albarkatun ƙasa, hasken rana mai yawa da kuma ƙwararrun injiniyoyi da za su iya samar da su a cikin gida.

Sabuwar yarjejeniyar ta yi daidai da manufar gwamnatin tarayya na ƙarfafa masana’antu da kuma mayar da Nijeriya cibiyar masana’antu a nahiyar Afirka.

Shugaban BPP ya kuma jaddada cewa za a tsaurara bin ƙa’idojin sayen kaya, inda ya ce ba za a ƙara amincewa da ayyuka ba sai sun cika sharuddan amfani da kayayyakin cikin gida.

Idan aka aiwatar da wannan shiri yadda ya kamata, ana sa ran haɗin gwiwar NASENI da REA zai sauya fuskar fannin makamashin sabuntawa a Nijeriya, daga dogaro da shigo da kaya zuwa iya kera da kuma fitar da su zuwa ƙasashen waje, tare da taimakawa wajen cimma burin samar da wutar lantarki ga kowa nan da shekarar 2030.

By ukarofi