Sabuwar ɓarkewar zazzaɓin Lassa ta halaka babban likita a Benuwe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani babban likita da ke aiki da ƙungiyar APIN a ƙaramar Hukumar Konshisha ta Jihar Benuwe ya rasu bayan ya kamu da cutar zazzaɓin Lassa.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jinƙai na Jihar Benuwe, Dakta Paul Ejeh-Ogwuche, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin a Makurdi, inda ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da marigayin tare da ƙarfafa matakan sa ido domin daƙile yaɗuwar cutar.

A cewar kwamishinan, marigayin ya shafe sama da makonni biyu yana fama da rashin lafiya kafin yanayinsa ya tsananta.

Ya ce, mutuwar likitan ta zo ne a daidai lokacin da jihar ke daf da samun sanarwar cewa ta kuɓuta daga cutar zazzaɓin Lassa.

“Mun sake samun sabon ɓullar cutar zazzaɓin Lassa a jihar. Marigayin likita ne, kuma an yi jana’izarsa a ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026. Yana aiki da gidauniyar APIN a ƙaramar Hukumar Konshisha, amma asalinsa daga ƙaramar Hukumar Kwande yake,” inji Dakta Ejeh-Ogwuche.

Ya ƙara da cewa, marigayin ya yi ta fama da cutar na tsawon lokaci ba tare da samun sauƙi ba, har sai da wani abokinsa ya yi zargin cewa alamomin da yake nunawa suna kama da na zazzaɓin Lassa.

“An gudanar da gwaji kuma sakamakon ya nuna cewa yana ɗauke da cutar zazzaɓin Lassa,” inji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa lokacin da aka nemi kwantar da marigayin a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi, ya nemi a ci gaba da kula da shi a gida ta hanyar magunguna da allurai.

Sai dai ya ce hukumomin lafiya sun nace cewa dole ne a kai shi asibiti domin a yi masa cikakken bincike da kulawa.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa marigayin yana fama da matsalolin ƙoda tun kafin kamuwarsa da cutar.

“Saboda haka ne aka tura shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos a Jihar Filato, inda daga bisani ya rasu,” inji kwamishinan.

Ya ce an dawo da gawarsa jihar Benuwe kuma aka yi masa jana’iza bisa ƙa’idojin da Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC) ta tanada game da binne waɗanda suka mutu sakamakon cututtuka masu yaɗuwa.

Bayan sake ɓullar cutar, kwamishinan ya ce ma’aikatar lafiya ta ƙara zage damtse wajen wayar da kan jama’a tare da sake kunna dukkan matakan gaggawa da ake amfani da su wajen yaƙi da cutar.

Ya bayyana cewa, an kuma sanya cibiyoyin lafiya cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon sabbin gargadi kan wasu cututtuka masu yaɗuwa, ciki har da Ebola.

“Muna ci gaba da wayar da kan jama’a, duba shirye-shiryen cibiyoyin lafiya, da kuma ƙarfafa sa ido a ko ina. Haka kuma mun fara binciken wannan sabon lamari tare da bin diddigin duk wanda ya yi hulɗa da marigayin,” inji Dakta Ejeh-Ogwuche.

Hukumomin lafiya na jihar sun yi kira ga jama’a da su gaggauta zuwa asibiti idan suka fara jin alamomin zazzaɓi mai tsanani ko wasu alamomin da suka yi kama da na zazzaɓin Lassa domin samun kulawar gaggawa.

By ukarofi