Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kuɗin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu ƙwarai daga kusan Naira tiriliyan 2.3 a farkon shekarar 2025 zuwa ƙasa da Naira tiriliyan 90 a shekara guda bayan haka.
Wannan ci gaba, a cewar gwamnati, ya samo asali ne daga bunƙasar matatun mai na cikin gida da kuma ƙara yawan man da ake tacewa a ƙasar.
Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Makamashi, Olu Verheijen, ce ta bayyana hakan yayin taron Ranar Makamashi na ƙungiyar Kasuwancin Nijeriya da Birtaniya na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Legas.
A cewar rubutaccen jawabin da aka gabatar a taron, samar da man fetur a cikin gida ya tashi daga kusan babu komai a shekarar 2023 zuwa kusan lita miliyan 48 a kowace rana a halin yanzu, inda mafi yawan man da ’yan Nijeriya ke amfani da shi yanzu ake tace shi a cikin ƙasar.
“Wannan shi ne karo na farko cikin tsawon zamani da mafi yawan man fetur da ’yan Nijeriya ke amfani da shi ake tacewa a cikin gida,” inji Verheijen.
Ta bayyana cewa wannan ci gaba ya rage matuƙar buƙatar amfani da kudin ƙasashen waje da ake kashewa wajen shigo da mai, lamarin da ya taimaka wajen rage matsin lamba kan darajar Naira.
A cewarta, tsawon shekaru, kowace jirgin mai da ake shigo da shi daga waje na ƙara matsin lamba kan samun dalar Amurka, wanda ke dagula tattalin arziki. Amma da zarar an ƙara tace mai a cikin gida, wannan matsin ya ragu sosai.
Verheijen ta kuma bayyana cewa tsaron makamashi da daidaiton kuɗi suna da alaƙa kai tsaye, tana mai cewa rage shigo da mai ya taimaka wajen inganta hangen nesa na tattalin arzikin ƙasar.
A ɓangaren samar da ɗanyen mai, ta ce Nijeriya ta samu ci gaba wajen dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari, inda aka samu matsakaicin samar da ganga miliyan 1.64 a kowace rana a shekarar 2025.
Wannan adadi, a cewarta, ya nuna ƙarin ganga kusan 400,000 a kowace rana idan aka kwatanta da matakin shekarar 2023, kuma shi ne mafi girman matakin samarwa a yankunan cikin ƙasa cikin shekaru ashirin.
Ta kuma bayyana cewa an kammala saye da sayar da kadarorin kamfanonin mai na ƙasashen waje da suka kai sama da dala biliyan 4, lamarin da ya ƙara bai wa ’yan Nijeriya damar shiga harkar mai a cikin gida, yayin da manyan kamfanonin mai na duniya suka koma kan hako mai a teku mai zurfi da kuma harkar iskar gas.
A cewarta, yanzu ana samun ingantaccen aiki a bututun jigilar mai, yayin da kuma aka rage matuƙar ayyukan tace mai ba bisa ƙa’ida ba. Ta ce kowace ganga da aka ƙara samarwa na da muhimmanci ga kuɗaɗen shiga, ayyukan yi da kuma ƙarfafa tarayyar ƙasa.
Ta kuma bayyana cewa a shekarar 2023, fannin mai da iskar gas yana cikin matsanancin hali sakamakon matsalar tallafin mai da rashin daidaiton musayar kuɗi da ƙarancin samarwa.
Sai dai ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara ne da matakan gyara, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma sake fasalin kasuwar canjin kuɗi.
A cewarta, duk da wahalar da matakan suka haifar, sakamakon ya fara bayyana, inda kuɗaɗen shiga na tarayya ya kai kusan tiriliyan N21 a shekarar 2024, daga kusan tiriliyan N12 a 2023.
Ta ƙara da cewa duk da sassauta dokoki a ɓangaren kasuwar mai ta ƙasa, gwamnati ta yi nasarar hana matsalar dogayen layukan mai da aka saba fuskanta a lokutan ƙarancin fetur a baya.
