
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a ƙauyen Ruwan Bore na Ƙaramar Hukumar Talata Mafara sun shiga firgici da jimami bayan wani mummunan harin ‘yan ta’adda da ya yi ajalin mutane 17 a ranar Juma’a.
Bayan harin, Shugaban ƙaramar hukumar, Yahaya Yari ya caccaki Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle bisa rashin cika alƙawuran da ya yi wa sojoji a jihar.
Wannan al’amarin ya haifar da damuwa akan rashin tsaro a Jihar Zamfara, inda mazauna suka fito zanga-zanga tare da nuna adawarsu akan ƙamarin rashin tsaron wajen tare babban titin Sakkwato zuwa Gusau na tsawon sa’o’i.
Da yake jawabi yayin jana’izar mamatan na Ruwan Bore, Hon. Yari ya yi kira ga Matawalle da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu rahoton halin da al’ummar yankin suke ciki, yana mai cewa al’amarin na kwanan nan ya nuna cewa har yanzu jama’a na fama da matsalolin hare-haren ‘yan ta’adda.
Ya kuma tunatar da kalaman Matawalle na kwanan nan cewa za a tura dakarun tsaro guda 10,000 zuwa jihar domin yaƙar ‘yan bindiga. A cewarsa, har yanzu babu sojan da aka tura.
Yari ya kuma gargaɗi ministan da cewa “ya sani kowa zai tsaya a gaban Allah ya yi bayani a ranar sakamako”.
Ya ƙara da cewa, yanzu lokaci ne da ya kamata a jingine maganar siyasa tare da mayar da hankali wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Zamfara, yana mai cewa cigaba da fuskantar hare-hare ga al’umma karya gwiwa ne a gare su akan jagororinsu.
Tuni dai jagororin al’umma a Talatan Mafara suka ce suna buƙatar Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki, inda suka yi gargaɗin cewa dukkan wani jinkiri akan haka ka iya sanya al’umma cigaba da gudanar da zanga-zangar nuna gazawar gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
