Rundunar sojoji ta yi wa manyan jami’anta garambawul, ta naɗa sabbin kwamandoji

Spread the love

Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da sauya muƙaman manyan dakarun rundunar a sassa daban-daban na ayyuka, jagoranci, horaswa da gudanarwa.

Rundunar ta ce, matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta aikin sojoji, ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma bunƙasa shirin tunkarar sabbin barazanar tsaro da ke addabar sassan ƙasar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’a ta riƙo ta rundunar, Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Asabar.

Sabbin naɗe-naɗen sun haɗa da nada Manjo Janar WM Dangana a matsayin kwamandan Runduna ta 3 da kuma kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation ENDURING PEACE, yayin da Manjo Janar EI Okoro ya zama kwamandan Runduna ta 6 da kuma shugaban ɓangaren sojojin ƙasa na Operation DELTA SAFE.

Kazalika, Rundunar ta kuma naɗa sabbin kwamandoji a wasu briged da sassan ayyuka na musamman domin ƙarfafa jagoranci da shirin ko-ta-kwana.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai kwamandan Nigerian Army Space Command da kuma Daraktan Leken Asiri da Tsaro a Hedikwatar Tsaro, domin bunƙasa amfani da fasaha da inganta ayyukan tsaro.

A fannin horarwa da ci-gaban ƙwarewar jami’ai kuwa, an naɗa sabbin shugabanni a Kwalejin Tsaro ta Ƙasa da Makarantar Sulke ta Sojoji da Makarantar Samar da Kayayyaki da Sufuri, da kuma Hedikwatar Horaswa da Tsare-tsaren Sojoji.

Babban Hafsan Sojin ya buƙaci sabbin hafsoshin da aka naɗa su nuna ƙwarewa, nagartaccen jagoranci da jajircewa wajen kare ikon Nijeriya, da martabar ƙasarta, tare da tallafa wa hukumomin farar hula wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Har ila yau, rundunar ta ce za ta cigaba da sauye-sauyen da za su gina ƙwararriyar rundunar soji mai cikakken shiri don fuskantar ƙalubalen tsaro na yanzu da na gaba a ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply