Gwamnatin Trump za ta yi matuƙar sanya ido a zaɓukan Nijeriya na 2027, inji ɗan majalisar Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya ce gwamnatin ƙasar za ta bibiyi tare da sanya ido a babban zaɓen Nijeriya na 2027, yana mai cewa shi da Shugaba Donald Trump za su kasance masu kula da yadda za a gudanar da zaɓen.

Moore, wanda ɗan jam’iyyar Republican da ke wakiltar Virginia ta Yamma ne, ya bayyana haka ne a wata hira ta gidan talabijin na Noire a rana Lahadi a lokacin da yake amsa tambayoyi akan zaɓen Nijeriya da ke tafe.

A cewarsa, Washington za ta kula sosai da hanyoyin da za bi wajen gudanar da zaɓen don tabbatar an yi sahihin zaɓe a ƙasar.

Ya kuma ce, majalisar wakilan Amurka na yunƙurin gabatar da ƙudurin da ya shafi hukunce-hukuncen Nijeriya musamman akan al’amuran addini da tallafin tsaro daga Amurka.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa, ƙudirin ya ƙunshi muhimman al’amuran da za su taimaka wajen ƙarfafa alaƙar Amurka da Nijeriya a nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply