‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya tara a hanyar Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu da ake zargin ɓarayin daji ne sun toshe hanyar Bakori zuwa Guga a jihar Katsina, inda suka sace matafiya aƙalla tara bayan sun dawo daga kasuwa ta mako-mako, in ji mazauna yankin.

An rawaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yamma ranar Juma’a a garin Dawan La’ila, sun toshe wani sashe na hanyar da ta haɗa al’ummomin Bakori da Guga, inda ‘yan bindigar suka tare motar da ke ɗauke da fasinjojin waɗanda suka dawo daga kasuwar Bakori.

Wani shugaban al’umma, Mahadi Ɗanbita, ya shaida wa majiyar Blueprint Manhaja a wata hira ta wayar tarho a ranar Asabar cewa maharan sun tsayar da motar suka yi awon gaba da fasinjoji tara.

Ya ce huɗu daga cikin waɗanda aka sace mazauna Guga ne yayin da sauran biyar suka fito daga Kakumi, wata al’umma da ke maƙwabtaka mai nisan kilomita tara.

A cewar Mallam Ɗanbita, waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun je cin kasuwar Bakori ta mako-mako lokacin da harin ya faru.

Ya ce mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun ƙwace wa fasinjoji kuɗi, wayoyin hannu da sauran kayayyaki masu daraja.

“Sun kai hari kan mutanen da ke dawowa daga kasuwa. Sun yi garkuwa da mutane tara. Har yanzu muna tattara bayanai daga iyalan da abin ya shafa da kuma wasu mutanen da suka samu nasarar tserewa,” in ji Mallam Ɗanbita.

Ya ƙara da cewa mutanen yankin sun bayar da rahoton cewa an kashe mutum ɗaya sannan wani ya ji rauni a lokacin harin, koda yake Manhaja ba ta iya tabbatar da waɗannan ikirarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Mallam Ɗanbita ya ce daga baya an kai motar da aka kai wa harin zuwa cibiyar kula da lafiya ta farko ta Guga.

Ya kuma bayyana sunayen mutane huɗu da aka ce suna cikin wadanda aka sace. Sun haɗa da: Sagir Mani Ɗanmadami, Babangida Ɗangwaggo, Bala Magaji da Abdullahi Muh’d Dabo.

Sai dai majiyarmu ta bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina bata yi ƙarin haske ba game da harin.

By ukarofi

Leave a Reply