Sauye-sauyen da ake ci gaba da aiwatarwa a hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ƙarƙashin jagorancin Alhaji Faisal Mahmud Kabir, sun fara haifar da gagarumin sakamako, inda jami’an hukumar ke nuna ƙwarewa, kishin ƙasa, tausayi da kuma sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarori masu yawa wajen tabbatar da bin dokokin zirga-zirga tare da rungumar tsarin aiwatar da doka cikin mutuntaka da jin ƙai.
Ɗaya daga cikin nasarorin da aka samu kwanan nan ita ce kama wata babbar mota (trailer) da ke ɗauke da kayan maye zuwa Jihar Kano, inda dokokin jihar suka haramta sayarwa da shan barasa. Hukumar ta bayyana wannan aiki a matsayin wata shaida ta jajircewarta wajen tabbatar da bin dokokin da ke aiki da kuma kare zaman lafiya da ɗabi’un al’umma.
A wani lamari da ya samu yabo daga jama’a, wani jami’in KAROTA ya nuna abin koyi na tausayi yayin da yake gudanar da aikinsa na hukuma.
Jami’in ya tare wani direba bisa karya dokokin zirga-zirga. A yayin tattaunawar, direban ya bayyana cewa yana cikin gaggawar neman jini ne domin ceton rayuwar ‘yarsa da ke kwance cikin mawuyacin hali a asibiti, inda likitoci suka buƙaci a yi mata ƙarin jini cikin gaggawa. Ya roƙi jami’in da ya ba shi damar ci gaba da tafiya, yana mai bayanin cewa wannan gaggawar ce ta sa ya karya dokar hanya.
Maimakon ya yi watsi da bayanin direban, jami’in ya ɗauki matakin tantance gaskiyar lamarin. Bayan tabbatar da cewa yarinyar na kwance cikin mawuyacin hali a asibiti kuma tana buƙatar jini cikin gaggawa, jami’in KAROTA ya yanke shawara mai cike da jin ƙai ta hanyar ba da jininsa domin ceton rayuwar yarinyar.
Wannan gagarumin aiki na sadaukarwa ya samu yabo daga ma’aikatan lafiya da ke kula da yarinyar, tare da mahaifiyarta wadda daga bisani suka ziyarci hedikwatar KAROTA domin nuna godiyarta ga hukumar bisa rainon jami’ai masu ɗa’a, tausayi da kishin yi wa al’umma hidima.
Daga cikin manyan jami’an lafiya da suka ziyara ci KAROTA don nuna godiyar sun har da Dr Dalha Gwarzo na AKTH, Prof Mahmud A. Abbas DG KNCDC, Dr Usman Bashir DG KANO SACA da kuma Dr Rahila Muktar ES-KASCHMA dukkan su ‘yan kwamitin ba da gudunmawar Jini.
Da yake martani kan lamarin, Manajan Daraktan KAROTA, Alhaji Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa halayen da jami’in ya nuna suna nuna irin ƙimomin da shugabancinsa ke ƙoƙarin tabbatarwa a cikin hukumar baki ɗaya.
Ya sake jaddada aniyarsa ta ƙarfafa ƙwarewa da tarbiyyar jami’an hukumar ta hanyar ci gaba da shirye-shiryen wayar da kai, horo da gina kyawawan ɗabi’u. Ya ce wajibi ne aiwatar da dokokin zirga-zirga ya kasance ba kawai bisa ƙwarewa ba, har ma tare da tausayi da mutunta rayuwar ɗan Adam.
Alhaji Faisal Mahmud Kabir ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa cikakken goyon bayan da yake bai wa KAROTA, yana mai cewa nasarorin da hukumar ke samu a halin yanzu sun samo asali ne daga manufofin gwamnatin da suka mayar da hankali kan jin daɗin al’umma.
Ya ce jajircewar gwamnan wajen nuna tausayi, adalci da kula da walwalar al’umma, musamman masu buƙata, na ci gaba da zaburar da hukumomin gwamnati su sanya jin ƙai da mutuntaka a sahun gaba wajen gudanar da ayyukansu.
A ƙarshe, Manajan Daraktan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa KAROTA za ta ci gaba da tabbatar da tsaron lafiyar masu amfani da hanyoyi tare da kiyaye mafi girman matsayi na ƙwarewa, riƙon amana da tausayi wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.
