Kofin Duniya: Norway ta kai wasan dab da na kusa da na ƙarshe a karon farko bayan doke Brazil

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Norway ta shiga sahun ƙasashen da suka kafa tarihi a harkar wasan ƙwallon ƙafa na zamani bayan doke Brazil da ci 2 da 1 a wasan zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya na 2026.

Wannan shi ne karo na farko da Norway ta kai zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe a gasar, kamar yadda ita ma Brazil wannan shi ne karon farko da aka cire ta zagayen tun a 1990.

Da fari, ɗan wasa Bruno Gumarães ne ya zubar da bugun fenarati bayan dogon lokaci da sashen binciken VAR ya ɗauka yana nazari akan al’amarin.

Earling Haaland ya samu damar zura ƙwallon farko a wasan ne a minti na 79 da ka bayan samun ƙwallon daga bugun kusurwa ta hannun Andreas Schjelderup.

Bayan minti 11 ne ya sake samun damar zura ta biyu yayin da ake gab da kammala wasan.

Duk da cewa Brazil ta cigaba da yunƙurin farkewa, hakan bai samu ba domin kuwa ɗaya kaɗai ta samu damar zurawa ta hannun ɗan wasa Neymar a bugun fenarati.

A yanzu dai Norway za ta kara da Ingila da ta cire Mexico a gasar a zagaye na gaba.

By Babaji

Leave a Reply