An yi kira ga gwamnatin Katsina ta binciki yadda gobara ta lashe cibiyar kula da lafiya ta Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Ƙungiyar cigaban Funtua a Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin Katsina da ta binciki yadda Gobara ta laƙume cibiyar kula da lafiya na Funtua tare da ɗaukar mataki na gyaran cibiyar duba da mahimmancin da take da shi wajen kula da lafiyar al’ummar yankin.

Shugaban ƙungiyar Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira bayan shi da ya’yan kungiyar suka ziyarci cibiyar wadda ita ce ta biyu bayan babban asibitin Funtua.

Ya ce gobarar ta lashe ginin cibiyar gaba ɗaya tare da duk abinda ke ciki.

Ya ce cibiyar ita ce ta biyu bayan babban asibitin Funtua inda mutanen ƙananan hukumomin da ke kusanci da yankin Funtua har ma da wasu garurruwa na jihohin Kaduna da Zamfara ke zuwa neman lafiyar su.

Kwamred Suleiman ya zargin hukumar kashe gobara ta gaza wajen samar da motar kashe gobara ta kai ɗauki a yayin da cibiyar ke cin wuta.

Kan haka ne yayi kira ga gwamnatin Jihar da ta kafa kwamitin bincike don gano gazawar hukumar kashe gobara a yankin na yin yunƙurin kashe wutar da ta laƙume kayayyakin kiwon lafiya na miliyoyin Naira.

By ukarofi