Daga JOHN D WADA a Lafiya
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da wata babbar masana’antar sarrafa lithium ta Najeriya wadda gwamnatin jihar Nasarawa ta gina inda ya bayyana cewa harkar ma’adinai za ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin gwamnatin tarayya na sauya fasalin tattalin arziki da samar da ayyukan yi da kuma sanya Najeriya cikin manyan ƙasashe masu fafatawa a kasuwar ma’adinai ta duniya.
Da yake wakiltar shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen ƙaddamar da masana’antar Diamond New Energy Projects ta sarrafa lithium a ranar Alhamis, Shettima yace wannan jarin ya nuna ƙaruwar ƙwarin gwiwa kan sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya da kuma yawan ma’adinai da ƙasar ke da su.
Ya jaddada cewa Najeriya dole ne ta daina fitar da ɗanyen ma’adinai ta koma yin sarrafawa a cikin gida domin samun fa’ida mai yawa daga tattalin arziki.
“Abin da ke sauya ƙasa shi ne ƙudurin canzawa daga tono zuwa sarrafawa, daga samun damar zuwa samarwa, daga ɗanyen kaya zuwa kayan da aka ƙara musu ƙima, da kuma daga jarin da ya ke ware zuwa tsarin masana’antu da suka haɗu,” in ji mataimakin shugaban ƙasan.
A cewarsa Najeriya ta tsaya a wani muhimmin lokaci kuma dole ne ta yi amfani da yalwar ma’adinai da take da su domin bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi da gina ƙwarewa a cikin gida. Ya bayyana ma’adinai a matsayin ginshiƙin fasahar zamani, yana mai cewa babu wani ci gaban fasaha da zai yiwu ba tare da ma’adanai masu mahimmanci ba kamar lithium da zinari da tagulla baƙin ƙarfe da kuma ma’adanai masu wuya.
Shettima yace ƙaddamar da wannan masana’anta ya nuna ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Najeriya da kuma tsarin sauyi na gwamnatin Tinubu.
“Wannan yana nufin cewa Najeriya ta shirya ta shiga harkar ma’adinai ta duniya bisa sharuɗan da za su samar da ayyuka, gina ƙwarewa da ƙarfafa ‘yan kasuwa na cikin gida da kuma faɗaɗa tushen samar da kayayyaki,” in ji shi.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa sanya Jihar Nasarawa ta zama ɗaya daga cikin wurare na farko wajen jawo jarin harkar ma’adinai da sarrafa su yana mai cewa jihar misali ce wajen gudanar da harkar hakar ma’adinai bisa alhakin da ya dace.
A nasa jawabin gwamna Sule yace kafa wannan masana’antar ta lithium ta ƙara tabbatar da cewa Nasarawa na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke da albarkatu masu yawa don jawo zuba jari.
Ya yi kira ga masu zuba jari na cikin gida da waje da su yi amfani da yalwar ma’adanai da jihar ke da su da kuma kusancinta da babban birnin tarayya Abuja.
Ministan cigaban ma’adinai Dr. Dele Alake a nasa ɓangaren yace sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi sun inganta ƙwarin gwiwar masu zuba jari a fannin ma’adinai na Najeriya.
Ya bayyana masana’antar sarrafa lithium a matsayin shaida kan jajircewar gwamnati wajen haɓaka ƙarin ƙima da ci gaban masana’antu maimakon ci gaba da fitar da ɗanyen ma’adinai.
Haka kuma sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma Ahmed Wadada ya roƙi kamfanin da ya faɗaɗa aiki daga sarrafa ma’adinai zuwa kera baturan lithium a cikin gida domin samun ƙarin ƙima da samar da ayyuka da ƙarfafa ƙarfin masana’antu na Najeriya.
Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Mohammed Ahmed shima yace wannan aikin zai samar da ayyukan yi da ƙara kudaden shiga na cikin gida da kuma haɓaka harkokin kasuwanci a yankin yana mai tabbatar wa masu zuba jari kan yanayin zaman lafiya.
Da yake magana a madadin masu zuba jari jakadan Jiuling da Canmax wato Yu Chongqiang yace kamfanonin sun zaɓi Nasarawa ne saboda manufofinta masu sauƙaƙe wa masu zuba jari. Ya bayyana shirinsu na faɗaɗa ayyuka a Najeriya domin biyan buƙatar lithium dake ƙaruwa a duniya.
A ƙarshe Sarkin Keffi Shehu Chindo Yamusa III wanda yayi jawabi a madadin Majalisar Sarakunan jihar Nasarawa ya yi maraba da wannan jarin yana mai cewa zai ƙarfafa matsayin Najeriya wajen sarrafa ma’adinai da ƙara musu ƙima tare da haɓaka tattalin arzikin ƙasar.
