Gwamnan Nasarawa ya miƙa sandan sarauta ga sabon Aren Eggon

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya miƙa sandar girma na musamman na sarauta ga Alƙali Ahmed Ubangari Alaku mai ritaya inda ya naɗa shi a hukumance a matsayin sabon Aren Eggon wato sarki mai daraja a faɗin Ƙasar Eggon.

Wannan naɗin sarautar mai ɗimbin tarihi ta zo ne kusan shekaru 40 bayan marigayi tsohon gwamnan Filato Solomon Lar ya fara ba da amincewa ta gargajiya ga wani Aren Eggon a lokacin da jihar ta Nasarawa ke cikin tsohuwar jihar Filato lamarin da ya zama muhimmin tarihi a cikin harkar sarautar Eggon.

Wakilin mu ya ruwaito cewa Ubangari Alaku ya hau kan karagar mulkin Aren Eggon ne a ranar 5 ga Mayu na 2023 bayan amincewar sarakunan masarauta da kuma tabbatar da zaɓinsa daga gwamnatin jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin da aka gudanar a Nasarawa Eggon Gwamna Sule ya buƙaci sabon sarkin da ya gudanar da ayyukansa bisa adalci gaskiya da tsoron Allah yana mai cewa sarakunan gargajiya suna da muhimmiyar rawa wajen mulki da zaman lafiya a cikin al’umma.

“Masarautan gargajiya abokan haɗin gwiwa ne da ba za a iya raba su da gwamnati wajen ci gaba ba,” in ji Sule. “Sune masu kiyaye al’adunmu masu haɗa kan jama’a da zaman lafiya da kuma masu shiga tsakani wajen warware rikici.”

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta cigaba da ƙarfafa masarautun gargajiya ta hanyar shigar da su cikin harkokin mulki inda ya ce irin wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen samar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Ya bayyana sabon Aren Eggon a matsayin mutumin da aka san shi da gaskiya da hikima yana mai cewa yana da ƙwarin gwiwa kan ikonsa na haɗa Ƙasar Eggon da kawo cigaba.

“Mai Martaba yana da hikima da gaskiya. Fitowarsa ya ba Ƙasar Eggon bege na ci gaba da bunƙasa,” in ji shi.

Sule ya kuma umurci sabon sarkin da ya yi amfani da matsayinsa wajen haɓaka zaman lafiya da tabbatar da mutunta tsarin dimokuraɗiyya gabanin zaɓen cike gurbin Sanatan Nasarawa ta Arewa da za a gudanar nan gaba.

Ya ambaci wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke yi a Nasarawa Eggon da kewaye ciki har da kasuwar zamani ta Nasarawa Eggon a hanyar Alizaga Hill-Wuyo-Wamba da kuma hanyar Nasarawa Eggon–Arugbadu.

A nasa jawabin kwamishinan ƙananan hukumomi da cigaban al’umma da harkokin masarautu Aminu Maifata yace fitowar Ubangari-Alaku ta biyo ƙa’idojin gargajiya bayan rasuwar marigayi Aren Eggon na da wato Dr. Bala Abaine-Angbazo.

Ya yaba wa gwamna kan gyaran fadar sarakuna a faɗin jihar tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da ba da goyon baya ga masarautun gargajiya.

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a nasa ɓangaren wato Aliyu Ibn-Aliyu yace wannan naɗi zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin mutanen Eggon da maƙwabtan su.

A cikin jawabinsa na godiya sabon Aren Eggon ya gode wa gwamna bisa amincewa da miƙa sanda mai alama na daraja yana mai alƙawarin mulki da adalci da jajircewa wajen zaman lafiya da cigaba.

“Na roki ’ya’ya maza da mata na Ƙasar Eggon mu haɗa hannu wajen gina Ƙasar Eggon mai ƙarfi, wadata da haɗin kai da Nasarawa mai zaman lafiya da Najeriya mafi kyau,” in ji shi.

Wakilin namu ya kuma rawaito cewa ɗimbin ‘ya’yan ƙabilar ta Eggon daga ciki da wajen jihar ne suka halarci taron karrama basaraken nasu da sandan girman dake cike da tarin tarihi cikin annashuwa.

By ukarofi

Leave a Reply