Lokacin da na ƙetare layin bauta, sai da na kalli hannuna domin tabbatar da ko ni ɗin ce – Harriet Tubman
(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
A makon da ya gabata mun soma bibiyan tarihin wata jaruma mai matuƙar girma a tarihin duniya, Harriet Tubman wadda aka haifa cikin ƙangin bauta, amma ta ƙi yarda rayuwarta ta ƙare a sarƙoƙin bauta. Mun bi sawun ƙurciyarta a Maryland, mun dubi yadda rayuwar bauta ta gina tsoro tun a lokacin ƙurciya, har zuwa mummunan rauni da ta samu a lokacin ƙurci wanda ya zama rauni da ya sauya mata yadda take kallon duniya, kuma ta mayar da rauni ƙarfi, sakamakon mayar da zafin raɗaɗin da take fama da shi kusan koyaushe addini, kuma hanyar nuna mata inda ya kamata ta bi don cetar kanta da al’ummarta.
Mun kuma ga yadda ta tsere daga bauta karon farko da yadda ta isa ƙasar ‘yanci, sannan muka kwana kan tambayar ko hankalinta ya kwanta ta ci moriyar ‘yancinta ba tare da waiwayen baya ba?
A wannan makon kamar yadda muka yi alƙawari za mu fara da amsar tambayar da muka kwana kanta, kafin mu ɗora da wasu waɗanda muke hasashen za su samar da ruwan kashe ƙishirwar masu karatu na daga rayuwar wannan jajirtaciyar gimbiyarmu ta wannan makon.
Kamar satin da ya gabata, Aisha Asas ce ke ɗauke da tarihin jajirtaciyar mace da ta farauto ‘yanci a lokacin da ba a tunanin zai iya samuwa, wato Harriet Tubman.
A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Me ya sa ta koma inda aka bautar da ita bayan ta samu ‘yanci?
Abin da zai bayar da mamaki kan lamarin rayuwar wannan baiwar Allah shi ne, duk da ta samu abinda da yawa daga cikin al’ummarta ba sa mafarkin samu, Harriet Tubman ba ta ɗauki tsayin lokaci don morar iskan ‘yanci ba, ta kasa mantawa da waɗanda ta baro a baya. Iyayenta, ‘yan uwa da kuma mutanenta da ta yi rayuwar sarƙa tare da su. Wannan tunanin ne ya rinjaye daɗin iskan ‘yancin da ta samu, don haka ta yi aniyyar komawa, don samun damar kai su ga daɗin da ta ɗanɗana a yanzu. Idan kuwa za a haikanto tafiyar za a iya cewa ba abu ne mai sauƙi ba, don haka wahalhalun da za ta shiga ba za su zama abin mamaki ba.
Yaushe ne ta fara jagorantar hanyar neman ‘yanci ga mutanenta?
Harriet ta fara jagorantar mutane cikin sirri daga kudancin Amurka zuwa Arewa. Ta yi amfani da hanyar da ake kira ‘underground railroad’, amma ba jirgin ƙasa ba ne, wata hanya ce ta sirri ta gidajen mafaka da masu taimako.
Ta yi tafiyar da ke cike da hatsari, ta samar wa wasu mafaka, ta ƙarfafa gwiwar wasu, haka ta zama jagorar da ba jimawa sunanta ya haskaka a tsakanin bayin da ke cikin ƙangin bauta. Ta ɗau tsayin lokaci kafin ta zama haske ga bayi, kuma barazana ga masu mallakar bayi.
Me ya sa take kallon ‘yancinta ba ‘yanci ba har sai tare da na wasu?
A lokacin da Harriet Tubman ta isa Philadelphia ta shiga sabon yanayi na rayuwa da ba ta taɓa shiga irinsa ba, ta fuska mai kyau. Babu mai iko da ita, kuma babu fargabar a siyar da ita, babu bulala, babu fargabar rabuwa da iyali a koyaushe. Saidai abin mamakin shi ne wannan natsuwar ba ta kawo mata cikakkiyar natsuwa ba.
Domin a duk lokacin da ta rufe ido hoton waɗanda suka rage a baya take tunawa, takan tuna iyayenta, ‘yan uwanta da dubatan mutanen da ke rayuwa a ƙarƙashin tsarin da ta tsere daga gare shi. Wannan tunanin ne ya zama wani nauyi da ya fi sarƙar bauta nauyi a gare ta.
Anan ne Harriet ta fahimci wani abu kuma har ta kai ga furtawa, wato ‘yancin da aka keɓe maka kai ɗaya bai cika ma’anar ‘yanci ba. Da wannan ne ta yanke shawarar da ba ta zama mai sauƙi gare ta ba sai dai ta zama tubalin da ake ambata a duk lokacin da ake tarihin bauta.
Sanannen abu ne komawarta inda ta baro ba tafiya ce da zata kintace sauƙi a cikinta ba, domin ta shirya komawa inda ake neman rayuwarta, ko ta yi rai ko ta mutu bisa ƙudurinta na ceta sauran al’ummarta.
A karon farko ta fara ne da ceto danginta. Wanda tarihi ya nuna irin hatsarin da ke cikin hakan da kuma irin ƙalubalen da ta yi ta cin karo da su kafin nasarar. Wannan nasara ce kuwa ta buɗe hanya gare ta ta ceto sauran jama’ar da ke cikin wannan ƙangi na bauta.
Ta fara da ceto ƙanana da masu rauni daga cikin bayi, tana mayar da su Arewacin ƙasar, wasu kuma ta fitar da su zuwa Kanada. Tana amfani da tsarin hanyoyin sirri na gidajen ɓoye da ke bada mafaka da kuma hanyoyin da za a iya fita da bayi ba tare da an kama su ba. ƙudurinta na kai ‘yan uwanta da ke cikin bauta zuwa yankin ‘yanci ya zama babban makamin da ta yi yaƙi da shi tsayin lokaci.
Harriet Tubman ta zama ɗaya daga cikin fitattun jagororin wannan tsarin, saidai bambancinta da saura shi ne, ba ta tsayar da taimakonta daga nesa ba, ita da kanta take shiga cikin yankin da bayin suke mai cike da hatsari tana kai su ga tudun tsira. Wannan ne ya sa ta yi fice fiye da sauran takwarorinta masu rajin kuɓutar da bayi daga ƙangin azaba.
Wacce ce babbar nasarar da ta samu kawowa lokacin?
Yayin da Harriet Tubman ke ƙara jajircewa kan abinda ta ɗaukarwa kanta alƙawarin yi, ta samu babbar nasara ta ceto mutane da dama, saidai babbar nasarar mai tafe da ƙalubale ita ce yadda ta yi nasarar dasa tsoro a zukatan masu mallakar bayi, ganin yadda duk ta tafi sai ta dawo, kuma duk ta dawo sai ta yi nasarar ficewa da wasu bayin ba tare da an kamata ba.
Take suka fara shirin ganin sun kawar da ita, suka ƙara kuɗin lada ga duk wanda ya kawo masu ita da rai ko a mace. Saidai abinda ya fi tsorata su shi ne yadda duk da ƙarin matsin lamabar da suke yi da ƙudurin kamo ta a kullum tamkar suna zugata, domin har ƙara yawan shige da ficen ta yi. Hakan kuwa ya zama wani ƙarfi ga bayin da suka mallaka inda suka rage tsoro tare da faɗar a’a ga cin zarafin da suke masu wanda a can baya ba su musuntawa.
Hakan ya sa ta wani ɓangare ta zama allon kwaikwayo, dalilin yawaitar baynin da ke yunƙurin tserewa don kare kansu wanda suke fatan su yi nasara kamar yadda ta yi, ko su ci karo da ita a hanyar yin hakan.
Wani ɓangare kuwa suke zuba ido tare da kasa kunne don jin ta inda za ta ɓullo ko saƙonta ya iso, don a shirye suke su bi hanyar da suke tsoro cikin ƙarfin hali matuƙar zata jagorance su.
Yaushe ta shiga yaƙin basasa?
Lokacin ya yaƙin basasa ya ɓarke a Amurka, Harriet ta shiga sabon mataki na rayuwa, inda ta soma da aiki tare da rundunar Union, inda ta yi aiki a matsayin ma’aikaciyar jinya, mai tattara bayan sirri da kuma leƙen asiri.
Ilimin da ta samu daga rayuwar bauta da tafiya cikin dazuka ya zama makami mai ƙarfi da ke riƙe a hannunta. Ta fahimci ƙasa, motsin mutane da dabarun ɓoye kai fiye da yawancin sojoji. Wannan ne ya sa sunanta ya sauya ko kuma ince ya ƙaru, domin a wannan lokaci mutane ba suna kallon ta a matsayin mai ceton bayi ba kawai, ta zama wata ginshiƙi mai tasiri a yaƙin da ake gwabzawa.
A shekarar 1863, Harriet Tubman ta taka muhimmiyar rawa a Combahee River Raid a South Carolina, inda ta taimaka wajen tattara bayanan sirri da tsara farmakin da ya kai ga lalata ƙadarorin mamallakan bayi.
A wannan farmaki, an kuɓutar da sama da bayi 700 a lokaci guda. Wannan ya zama ɗaya daga cikin manyan nasarorin kuɓutar da bayi a tarihin Amurka.
Wannan abin ya tabbatar da cewa, Harriet Tubman ba kawai jagora ce da ke ɓoye tana bada gudunmuwa ba, ta kasance mai tasiri a fili a cikin manyan sauye-sauyen tarihi.
Bayan nasara shin waɗanne irin ƙalubale ne ta ci karo da su?
Idan mai karatu na biye da mu cikin fahimta, zai fahimci cewa rayuwar Harriet Tubman tun a farkon ta akan ƙalubale ta ginu, kuma duk wata nasara da ta samu za a iya hango ƙalubalen da ke tattare da ita.
Duk da irin girmanta a tarihi, rayuwar Harriet Tubman ba ta taɓa zama mai sauƙi ba. Ta rayu da ciwon kai mai tsanani daga raunin da ta samu tun tana da ƙuruciya. Ta fuskanci talauci, wariyar launin fata, da wariyar jinsi. Ga uwa uba rayuwa cikin zullumin farautar rayuwarta a koda yaushe.
Ko bayan yaƙi, ta shafe shekaru tana fafutukar neman fansho saboda aikinta a soja, abin da ya nuna yadda duniya ba ta cika yin adalci ga waɗanda suka yi sadaukarwa.
Bayan kai ƙarshen yaƙin, Harriet Tubman ta zauna a Auburn, New York, inda ta ci gaba da taimaka wa marasa galihu da kuma fafutukar neman haƙƙin mata. Duk da talauci, ta ci gaba da rayuwa cikin hidima ga wasu.
Ta rasu a shekarar 1913, saidai abinda ta shuka ya ci gana da gudana. Sunanta ya ci gaba da zama alamar jarumta, sadaukarwa da neman ’yanci.
