
Iran ta yi gargaɗi ga dukkan jiragen ruwa da tankokin ɗaukar mai da ke bi ta Mashigin Strait of Hormuz cewa su yi amfani ne kawai da hanyoyin da hukumominta suka amince da su, tana mai cewa duk wanda ya saɓa zai fuskanci “martani mai ƙarfi cikin gaggawa.”
Sanarwar ta fito ne daga rundunar haɗin gwiwar sojojin Iran, wadda ta ce duk wani jirgin ruwa da ya kauce wa hanyoyin da aka tsara ko ya yi watsi da umarnin kewayawa zai iya jefa tsaron jirginsa cikin haɗari.
Gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran kan makomar zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz, wanda ke ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar danyen mai a duniya.
Masana sun bayyana cewa duk wani sabon tashin hankali a wannan mashigi na iya shafar kasuwannin makamashi da safarar mai a duniya, duk da cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta fara farfaɗowa a hankali bayan raguwar rikicin.
