‘Ku nuna mana hujjar’: Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da iƙirarin kashe tiriliyan N8 da ba su cikin wajen kasafin kuɗi

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa ta kashe sama da Naira tiriliyan 8 a wajen kasafin kuɗin shekarar 2026, tana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.

Ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce an yi wa kalaman wakilin Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a Najeriya, Christian Ebeke, mummunar fassara.

Oyedele ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da abin da ake kira “kasafin kuɗi na ɓoye”, yana mai jaddada cewa duk kuɗaɗen gwamnati ana kashe su ne bisa dokokin kasafin kuɗi da majalisar tarayya ta amince da su.

Ya ce ayyukan manyan gine-gine da ke ɗaukar shekaru fiye da ɗaya ana aiwatar da su ne bisa tanadin doka, don haka bai kamata a ɗauke su a matsayin kashe kuɗi ba tare da kasafi ba.

Ministan ya ƙalubalanci masu wannan zargi da su fito da takamaiman ayyukan da aka aiwatar ba tare da amincewar majalisa ba, tare da gabatar da hujjoji masu inganci.

Zargin ya biyo bayan rahoton IMF da ya nuna cewa an kashe kuɗaɗe da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na GDP a wajen kasafi a shekarar 2025, lamarin da ya jawo suka daga wasu ‘yan adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da Peter Obi, waɗanda suka buƙaci a gudanar da bincike kan batun.

Sai dai Oyedele ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da bin ƙa’idojin gaskiya, riƙon amana da inganta tsarin tafiyar da kuɗaɗen jama’a.

By Babaji