
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Ingila ta sha da ƙyar a hannun Mexico a zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya na 2026 yayin da aka kammala wasan tsakaninsu da 3 da 2, lamarin da ya ba ta damar zuwa zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe.
Ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham ne ya zura ƙwallo biyu, wanda hakan ya ba ƙasar damar jan ragamar wasan, kana daga bisani Julian Quinones na Mexico ya goge ɗaya.
Bayan an sallami Jarell Quansah daga wasan ne sai Ingila ta samu damar ƙara ta uku a bugun daga kai sai mai tsaron gida ta hannun ɗan wasa Harry Kane. Daga bisani Julian Quinones ya zura guda wa Mexico kafin a tashi wasan.
A yanzu, Ingila za ta kara da ƙasar Norway ta su Erling Haaland a wasan dab da na kusa da na ƙarshe.
