Idan Tinubu ya lashe zaɓen 2027 sai na halaka ɗansa Seyi, inji DJ Chicken

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen mai nishaɗantarwa a Soshiyal Mediya da ake kira da DJ Chicken ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta sakamakon furta wasu kalamai masu hatsari akan sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu.

DJ’n ya yi haka ne a wani bidiyo ta shafinsa na Instagram duk da cewa daga bisani an goge shi, inda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ba zai lashe zaɓen da ke tafe ba.

Sannan, ya kuma yi barazana mai tayar da hankali akan ɗan Shugaban Ƙasar, Seyi Tinubu, inda aka ga yadda ɗan mediyar ya yi shiga irin ta kayan gargajiya da farin mayafi da sarƙar wuya yayin da yake wa al’umma jawabi.

“Tinubu ba zai lashe wannan zaɓen ba. Idan kuma ya yi nasara, zan halaka Seyi Tinubu”, inji shi.

Wannan faifai ya janyo faɗi-in-faɗa musamman wajen yin tir da allah-wadai da kalaman nasa acikin al’umma, inda wasu ‘yan Nijeriya ke bayyana su a matsayin marasa kan gado da ba za a lamunta ba.

Haka kuma, wasu da dama sun kirayi hukumomin tsaro da su gudanar da bincike akan al’amarin, suna masu gargaɗin hakan ka iya haifar masa da fuskantar hukunce-hukuncen shari’a da za su iya sanya shi cikin matsala.

Har zuwa lokacin kammala aikin haɗa wannan rahoto, iyalan Tinubu ko Fadar Shugaban Ƙasa ba su fitar da wani saƙo na musamman ba akan al’amarin.

By Babaji