Kofin Duniya: Su Messi sun yi waje da Misra bayan farfaɗowa a zagayen ‘yan 16

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Argentina ta yi nasara ana gab da tashi a wasa a karawarta da Misran su Mohammed Salah inda aka tashi 3 da 2 a zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.

Da fari dai Misra ce ta ja ragamar wasan bayan zura ƙwallo biyu a ragar Argentina, amma daga bisani zakaran ƙwallon ƙafa na Duniya Lionel Messi ya nuna bajinta yayin da wasan ya rage ƙasa da minti 20 a kammala.

A minti na 15 ne Yasser Ibrahim ya samu damar zura ƙwallon farko da ka daga bugun kusurwa. Bayan minti biyar, Argentina ta samu bugun fenarati, saidai mai tsaron gidan Misra ya ceci nasararsu yayin da Messi ya ɓarar da damar zura ƙwallon a raga, lamarin da ya zama ɗan wasa na farko a tarihin gasar da ya zubar da fenarati sau biyu a kaka ɗaya.

Yayin da aka shafe mintina 67 ana wasan ne ɗan wasa Mostafa Ziko ya ƙara ƙwallo ta biyu a ragar Argentina.

Bayan minti 12 ne Cristian Romero ya farke ɗaya daga ƙwallon da Messi ya jefa masa daga gefen dama na wajen zagayen 18.

A minti na 83 ne Messi ya samu damar mayar da wasan 2 da 2, sannan bayan ƙarin lokaci ne kuma Enzo Fernandez na Chelsea ya zura ta uku a minti na 93, lamarin da ya ba Argentina damar zuwa zagayen wasannin dab da na kusa da na ƙarshe.

A yanzu dai ƙwallon da Messi ya samu zurawa a yau ta ba shi damar cigaba da zama jagoran ‘yan wasa mafi yawan ƙwallaye a gasar, inda yake da guda takwas.

By Babaji