
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An shiga fargaba a yankin Ojo da ke cikin birnin Ibadan bayan wani rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna Yarabawa da Hausawa a safiyar yau Laraba, 8 ga Yuni, 2026.
An gano cewa, rikicin ya samo asalin ne sakamakon zargin kisan wani bayeraben bakaniken adaidaita sahu, wanda aka ce wasu ‘yan bola jari Hausawa ne suka sassare shi da dare har ya rasu.
Akan haka ne majiyoyi suka ce wasu matasa suka yi cincirindo a titina domin yin zanga-zanga akan zargin kisan bakaniken daga ‘yan bolan, lamarin da ya tayar da rikici tsakanin ɓangarorin biyu.
Bayan haka ne mutane da dama suka fice daga gidajensu saboda fargabar fuskantar mayar da martani daga matasan Hausawan.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wani sako na musamman ba akan al’amarin, amma an tura jami’an tsaro domin dawo da doka da oda da kwantar da hankula a yankin.
