Mun tallata Obasanjo da Jonathan, balle Tinubu — Hon. Ishak

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa harkar siyasa magana ce ta ra’ayi da fahimtar da mutum yake da ita, don haka babu wata matsala wajen tallata Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da sauran sanatoci da ‘yan majalisun jiha da na tarayya na jam’iyyar APC, domin su sake komawa kan kujerunsu a karo na biyu.

Hakan na zuwa ne bisa la’akari da cewa a baya an tallata tsofaffin shugabannin ƙasa biyu, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ba tare da la’akari da bambancin al’ada da addini ba. Saboda haka, a cewarsa, babu dalilin da zai hana tallata Bola Ahmed Tinubu, musamman kasancewar addini ya haɗa su.

Sabon Kwamishinan Ma’aikatar Jinƙai da Ci Gaban Al’umma ta Jihar Kano, Hon. Muntari Ishak Yakasai, ne ya bayyana hakan a lokacin da ɗumbin ‘yan uwa, masoya da magoya bayansa suka taru domin taya shi murnar komawarsa Ma’aikatar Jinƙai da Ci Gaban Al’umma ta jihar Kano, da ke kusa da fadar gwamnatin Kano, a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Haka kuma, ya yi alwashin haɗa kai da shugabannin ma’aikatar da ya samu a wurin, da sauran masu ruwa da tsaki, domin inganta ayyukan tallafa wa al’umma da rage raɗaɗin fatara da talauci a tsakanin al’ummar jihar Kano, daidai da manufar Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A ƙarshe, ya bayyana cewa akwai ƙauna da kyakkyawar fahimta tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya ce a shekarar 2014 zuwa 2015, shi ne ya yi masa Daraktan Yaƙin Neman Zaɓe lokacin da yake neman zama Sanatan Kano ta Tsakiya, amma daga ƙarshe ya ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso takara, kuma aka samu nasara.

Ya ƙara da cewa duk wani abu mai muhimmanci da Gwamna Abba yake yi, yana sanya sunansa a gaba, ciki har da kwamitin yaƙin neman zaɓen 2027. Saboda haka, ya yaba wa gwamnan bisa yadda yake cika alƙawari tun bayan haɗuwarsu da shi a jam’iyyar APC, tare da gode wa waɗanda suka taimaka wajen ganin ya zama kwamishina a wannan lokaci.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba shi wani muƙami da zai ba shi damar yi wa al’umma hidima, yana mai cewa shi ɗan al’umma ne, al’umma kuma tasa ce, don haka wajibi ne kowane ɗan siyasa ya kasance mai son al’umma da taimaka musu.

By ukarofi

Leave a Reply