Faɗaɗa harkokin intanet zai bunƙasa arzikin Nijeriya – NITDA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa, ya bayyana cewa sabbin dabarun samar da ababen more rayuwa da inganta ayyukan jama’a sun taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin fasahar zamani na Nijeriya, duk da ƙarancin wutar lantarki, hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Inuwa ya yi kira da a faɗaɗa fahimtar abin da ake nufi da bunƙasa ababen more rayuwa, yana mai cewa tattalin arzikin dijital na buƙatar zuba jari fiye da gine-gine kamar tituna da layukan dogo. Ya ce, “A yau muna rayuwa ne a zamanin fasahar zamani, saboda haka muna buƙatar gina manyan hanyoyin dijital da za su taimaka wajen zirga-zirgar bayanai kamar yadda muke da hanyoyin sufuri.”

Ya jaddada muhimmancin samar da ababen more rayuwa na dijital da kowa zai iya amfana da su, rage kuɗin samun damar intanet da kuma ci gaba da zuba jari a sabbin fasahohi domin hanzarta bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya, tare da tabbatar da cewa babu wani ɗan ƙasa da za a bari a baya. Inuwa ya bayyana hakan ne yayin halartar wani zama mai taken “Bunƙasa Tattalin Arziki Mai Haɗa Kowa a Zamanin Fasahar Dijital”, a taron ƙolin tattalin arzikin Nijeriya karo na 32 (NES#32), wanda Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arzikin ƙasa ta shirya.

Babban Daraktan ya jaddada muhimmancin faɗaɗa hanyoyin sadarwa na kamfanonin sadarwa, musamman a yankunan karkara da wuraren da har yanzu ba su samu isasshen sabis ba. Ya ce tarihin bunƙasar harkokin sadarwa a Afirka ya nuna yadda ƙirƙire-ƙirƙire da sabbin dabaru za su iya warware matsalolin da ake ganin ba za a iya shawo kansu ba.

Da yake waiwayen ci gaban ɓangaren sadarwa tun daga shekarar 2000, Inuwa ya tuna cewa a farkon lokacin, masu zuba jari da dama ba su da sha’awar saka kuɗaɗensu a harkar, saboda suna shakkar ko ’yan Afirka za su iya sayen wayoyin hannu da kuma biyan kuɗin amfani da su. Ya ce, babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne samar da damar amfani da fasahar ga kowa, rage kuɗaɗen da ake kashewa da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa zuwa yankunan karkara, domin kowane ɗan ƙasa ya samu damar taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin dijital.

Ya bayyana cewa samun damar sadarwa ya zama ginshiƙi wajen tabbatar da haɗa kowa cikin harkokin zamantakewa da tattalin arziki, musamman a wannan lokaci da fasahar basirar na’ura mai kwakwalwa (AI) ke ƙara tasiri wajen yanke shawara da gudanar da ayyuka a faɗin duniya. Inuwa ya ce, “Idan ba a wakilce ka ba, kuma ba ka da wata alama ta kasancewarka a duniyar dijital, fasahar AI ba za ta iya ganinka ko la’akari da kai yayin yanke shawara ba.”

Ya yi gargaɗin cewa rashin haɗa wasu al’ummomi cikin tsarin fasahar dijital na iya janyo rashin wakilcin al’adunsu, ƙimominsu da yarukansu a cikin sabbin fasahohin da ake ƙirƙira. Inuwa ya ce gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta himmatu wajen amfani da fasaha domin tabbatar da haɗa kowa cikin ci gaba da bunƙasa arzikin ƙasa. Ya bayyana cewa Shugaban ƙasa ya umurci Ministan Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani, da ya tsara wasu manyan shirye-shirye guda biyu da za su taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin sadarwa a faɗin ƙasar.

Shirye-shiryen su ne Asusun Samar da Sabis ga Kowa (USPF) da kuma shirin Project BRIDGE. A cewarsa, shirin USPF an tsara shi ne domin faɗaɗa hanyoyin sadarwa zuwa yankunan da ba su da isasshen sabis, ta hanyar kafa sabbin tashoshin sadarwa. Shi kuwa shirin Project BRIDGE na da manufar shimfiɗa kimanin kilomita 95,000 na wayoyin sadarwa masu amfani da zaren gilashi (fibre-optic) a faɗin Nijeriya.

Ya ce waɗannan shirye-shirye za su taimaka wajen samar da tsarin ababen more rayuwa da kamfanoni daban-daban za su iya amfani da su, ƙarfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu su zuba jari, da kuma rage kuɗin amfani da intanet mai sauri ga ’yan Nijeriya. Babban Daraktan NITDA ya sake jaddada cewa bunƙasa tattalin arzikin dijital na buƙatar zuba jari fiye da gine-ginen gargajiya kamar tituna da layukan dogo.

Ya ce, yayin da Nijeriya ke ƙoƙarin bunƙasa fasahar AI, wajibi ne ta zuba jari wajen gina cibiyoyin adana bayanai, samar da manyan na’urorin sarrafa bayanai da kuma masana’antun fasahar AI, domin ƙasar ta iya cin moriyar damar tattalin arzikin da wannan fasaha ke samarwa.

By ukarofi

Leave a Reply