An yi jana’izar waɗanda suka rasu a rikicin Gulma

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

An gudanar da jana’izar waɗanda suka rasu sanadiyyar faɗan makiyaya da manoma a garin Gulma a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu.
Da ya ke jawabi gabanin jana’izar, mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar a madadin gwamna Nasir Idris, ya bayyana alhinin gwamna bisa ga wannan lamarin.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan wadanda suka rasu tare da fatan Allah ya bai wa iyalan su da masarautar Kabi haƙurin jure wannan rashin .
Ya kuma tabbatar musu da cewa za a zaƙulo duk wanda ke da hannu a cikin wannan aika-aikar tare da hukumta su kamar yadda doka ta tanada saboda haka a yi haƙuri kada mutane su ɗauki matakin ɗaukar fansa da kan su.
A nasa jawabi, nai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, bayan jajantawa iyalan marigayan ya kuma ba su tabbacin za a yi bincike tare da kama duk wanda ke da hannu a cikin wannan kashe-kashen don hukunta su.

Shugaban Fulanin ya bayyana wannan a matsayin babban abin baƙin ciki ne da ya faru tsakanin su da manoma amma duk da haka ba zai hana su cigaba da zama tare ba.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar irin wannan nan gaba.
An an yi jana’izar makiyaya bakwai a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera.

By ukarofi