Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Manonan rani sun koka bisa yadda waɗansu tsuntsaye ke yi musu barazana ga amfanin gona a Kebbi.
Alhaji Musa Najada ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin manoma a jihar Kebbi ya bayyana cewa waɗannan tsuntsayen suna yi musu barazana ga amfanin gona musamman shinkafa a daidai wannan lokacin da suke daf da soma girbi wanda yanzu ya zama dole ga manomi ya yi Sallar asuba gona idan ba haka ba abinda zai samu sai dai rauno (ciyawa) saboda za ka ga ayarin su kamar hadari sun fi dubu kuma duk inda suka sauka kafin minti ɗaya ɓarnar da za su yi ba ƙarama ba ce.
Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo masu agaji saboda kada su yi asara, da ya ke mafi yawancin manonan ƙananan manoma ne suna rancen kuɗin da suke amfani da shi ne a bankuna da kamfunna da kuma hannun masu kuɗi.
Kwamishinan gona
Alhaji Shehu Ma’azu ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa tuni gwamna Malam Nasir Idris ya bayar da umarnin a nemo hanyar magance waɗannan tsuntsayen da suka addabi manoma musamman a yanki ƙananan hukumomin
Argungu, Birnin Kebbi, Bunza da sauran sassan jihar Kebbi da ke noman rani.
Ya ƙara da cewa wannan karon za a yi amfani da maganin da ke ɗaukar dogon lokaci kafin a sake samun afkuwar irin wannan iftila’i na tsutsaye. Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kebbi a shirye take don ɗaukar duk matakin da ya dace don kare alumma da dukiyoyin su.
