Kwastom ta kama bindigogin da aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya a Legas

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa (NCS) da ke Tin-Can Island a Legas, ta kama bindigogi da sauran kayayyakin da ake zargin wasu ɓata-gari sun shigo da su ta haramtacciyar hanya.

Majiyarmu ta ce sauran kayayyakin sun haɗa da rigunan sojoji haɗi da miyagun ƙwayoyi.

An ce Kwastom ta kama kayayyakin ne yayin da take duba kayayyakin da aka shigo da su daga ƙetare a tashar jirgin ruwa na Tin-can.

Sai dai babu cikakken bayani a kan ko an samu kama wani ko wasu da ke da alaƙa da kayayyakin.

Kama kayan na zuwa ne watanni takwas bayan fda Shugaban Hukumar, Adewale Adeniyi ya shaida wa manema labarai cewar, an kama wasu mutum biyu bisa zargin shigowa da bindigogi daban-daban guda 31 a Tin-Can.