RTEAN ta ƙaddamar da sabbin shugabannin Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar ma’aikatan motocin sufuri ta qasa (RTEAN) reshen jihar Legas ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar ta ƙasa.

Ku tuna cewa an dakatar da ayyukan RTEAN a jihar Legas sama da watanni 15. Bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi, an shawo kan lamarin wanda ya kai ga sake fasalin shugabannin ƙungiyar a jihar.

A lokacin da yake jawabi ga sabbin zaɓaɓɓun shugabannin a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Shugaban RTEAN, Musa Maitakobi ya umarcesu da su daina karya doka da oda da kuma kiyayewa a yayin gudanar da ayyukansu.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a bi hanyoyin lumana wajen magance matsalolin da ke faruwa a ƙungiyar maimakon yin zanga-zanga ko aikin dabanci.

“Ina son ku sani cewa ya zama wajibi mu kawar da dabanci ko ‘yan daba a duk wata tashar mota a faɗin tarayyar ƙasar nan. Amma don Allah a zauna lafiya, shi ne mafita don cimma burinku.”

Ya kuma buqaci sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar RTEAN reshen jihar Legas, mai martaba Oba Sulaiman Raji Adeshina, da ya gaggauta warware matsalolin da ke kan gaba a reshen jihar Legas.

A lokacin da yake gabatar da jawabin godiya, Oba Adeshina ya bayyana farin cikinsa da aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar RTEAN na jihar Legas.

Ya nanata muhimmancin yin aiki tare domin samun wa’adin mulki kyauta da cimma burin da aka sa a gaba.

“Na yi alƙawarin yin iya ƙoƙarina tare da ɗaukar RTEAN zuwa matsayi mafi girma. Ina roƙon dukkan membobin da masu gudanarwa su yi aiki tare a matsayin iyali ɗaya,” in ji shi.