Atiku, Yari da Ningi suna yunƙurin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A cikin makon nan ne dai jaridar The Nation ta samu labarin cewa ‘yan adawa na shirin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta tunkari jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓe mai zuwa.

Gabanin shekarar 2027, majiyoyi sun ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zacen shekarar da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da ƙudirin jam’iyyar da ake son a yi tare da haɗin gwiwar wasu ‘yan majalisar dokokin ƙasar.

An tattaro cewa, sansanin Atiku na taka-tsan-tsan da rashin haɗin kan da ke cikin babbar jam’iyyar adawa, yana tunanin cewa idan ta dage har 2027, jam’iyyar ba za ta iya kwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki ba.

Wata majiya ta shaida wa jaridar The Nation cewa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ya tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa kuma ya sha kaye a hannun Sanata Godswill Akpabio.

Tsohon shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa (NSF), Abdul Ningi, shi ma ya shiga tafiyar domin aiwatar da shirin.
Maganar Ningi a makon da ya gabata ta haifar da ruxani a majalisar dokokin ƙasar.

A cewar masu lura da al’amuran yau da kullum, akwai wani yunƙuri na maimaituwa abin da ya faru a shekarar 2013 inda wasu gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya suka yi wa jam’iyyar PDP tawaye tare da haxa kai da wasu jam’iyyu suka kafa jam’iyyar APC.

An kafa jam’iyyar APC mai mulki ne a watan Fabrairun 2013, bayan haxewar jam’iyyun Action Congress of Nigeria (ACN), Congress for Progressive Change (CPC), All Nigeria Peoples Party (ANPP) da wani vangare na All Progressives Grand Alliance (APGA) da abin da ake kira sabuwar-PDP.

Atiku wanda yana ɗaya daga cikin waxanda suka kafa jam’iyyar APC, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar a shekarar 2014 a hannun Janar Muhammadu Buhari.