Yadda Tinubu ya dakatar da shirin bada lamuni ga ɗalibai

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An ɗage ƙaddamar da shirin bayar da lamuni ga ɗaliban Nijeriya wanda aka shirya fara shi a gwamnatin Bola Tinubu, sa’o’i 48 gabanin ƙaddamarwa.

Akintunde Sawyer, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lamuni ta Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na AriseTV a ranar Talata.

Tun da farko an shirya farawa shirin ne a ranar Alhamis, amma an sake jingine ƙaddamar da shi, yayin da ake yin gyare-gyare don tabbatar da shirin cikin inganci ba tare da wata matsala ba, a cewar Sawyer. 

“Ba zan iya bayyana wani takamaiman kwanan wata ba. Amma muna tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki sun haxa kai wajen tabbatar da shirin, wanda zai ba mu damar aiwatar da shirin cikin kwanciyar hankali,” inji Sawyer.

A watan Yunin 2023 ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudirin kafa asusun ba da lamuni na xalibai (SLF), da nufin bayar da lamuni marar ruwa ga ‘yan Nijeriya masu neman ilimi.

Ƙudurin dokar da tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya gabatar, an shirya fara aiki ne tsakanin watan Satumba da Oktoban 2023.
Duk da cewa ba a cika wa’adin watan Oktoba ba, Tinubu ya ba da tabbacin cewa shirin zai fara ne a watan Janairu na 2024.

A watan Janairu, Ƙaramin Ministan Ilimi, Yusuf Sununu, ya tabbatar a yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) cewa shirye-shiryen da suka hada da kammala gidan yanar gizo na tsarin ba da lamuni na ɗalibai, tsare-tsaren fasaha, duk an kammala su don ƙaddamar da shirin.

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa da shugabannin ƙungiyar ɗalibai ta qasa (NANS) a ziyarar da suka kai fadar gwamnatin jihar cewa shirin zai fara aiki da zarar an kammala fadada shirin da zai haɗa da wasu abubuwa masu alfanu da dama.

By Editor