Ɗaliban Kuriga: Tinubu ya ƙi amincewa da tayin Sheikh Gumi na tattaunawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da tayin Sheikh Gumi na tattaunawa da ‘yan bindiga kamar yadda ya umurci hukumomin tsaro a ƙasar nan da su tabbatar an dawo da duk waɗanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Idan dai za a iya tunawa, an samu ƙaruwar satar mutane musamman a yankin Arewa maso Yamma na qasar nan a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, inda lamarin neman kuɗin fansa ke ƙaruwa.

Wasu gungun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da mutane 16 a yankin Gonin-Gora da ke cikin birnin Kaduna a jihar Kaduna, sun buqaci a biya su Naira tiriliyan 40 da Hilux ƙirar Toyota goma sha ɗaya da kuma babura 150.

Har ila yau, ‘yan bindiga a jihar Sakkwato sun yi garkuwa da almajirai 15, kuma sun kira iyalan, inda suka buqaci a biya su Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa kafin a sako su.

A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kusan 61 a ƙauyen Buda da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna ranar Litinin.

Amma a ranar Talatar da ta gabata ne wani malamin addinin Islama na Kaduna, Sheikh Gumi ya bayyana aniyarsa ta tattaunawa da ‘yan bindigar da suka sace ‘yan makaranta kusan 287 a Sakandaren gwamnatin Kuriga da kuma makarantun firamare na LEA a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

Gumi ya bayyana haka ne a wani yunquri na ganin an sako ‘yan makarantar da aka sace idan har Shugaba Bola Tinubu ya ba shi damar tattaunawa da ‘yan bindigar.

A cewar fitaccen malamin addinin Musuluncin, kada Tinubu ya maimaita kuskuren da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda ya qi tattaunawa da ‘yan fashi.

“Matsayin gwamnati na rashin tattaunawa da ‘yan bindiga wani matsayi ne mara daɗi.

“Shawarata ita ce gwamnati ta tattauna da ’yan bindiga ba wai kawai a sace yaran makarantar Kuriga ba, har ma a kowane hali.

“Har ila yau, ya kamata gwamnati ta yi amfani da hanyar da ta bi wajen sakin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2022 don sako yaran makarantar Kuriga da sauransu.

“A shirye nake in jagoranci cikakkiyar tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga. Aikina ne na addini in yi haka domin zaman lafiya.
“Ina fatan gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu za ta saurara ta hanyar tattaunawa da ‘yan bindigar saboda tsohuwar gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ƙi yin hakan,” in ji shi.

A baya Gumi ya shiga tsakano a madadin gwamnatocin jihohi domin kuɓutar da mutanen da ‘yan bindiga suka sace.

A watan Mayun 2021, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka yi garkuwa da su na Kwalejin Injin Daji ta Tarayya da ke Afaka a Jihar Kaduna, ya ce maimakon nuna yatsa ga Gumi da laifin hada baki da ‘yan fashi da suka addabi ƙasar nan, ya kamata ‘yan Nijeriya su yaba wa malamin tsoma bakinsa na neman a sako mutanen da aka sace a ƙasar.

Sai dai Tinubu a wani martani a kaikaice ga tayin da Gumi ya bai wa jami’an tsaro na ganin ba a biya kuɗin fansa domin cimma hakan ba.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a fadar gwamnati da ke Abuja, bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) na mako, wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Ya ce Tinubu ya jaddada matsayinsa na rashin biyan kuɗin fansa, duk da cewa ya ce su tabbatar an kuɓutar da duk waɗanda abin ya shafa, ba tare da wani uzuri ba.

Ya ce: “Kuna kuma tambaya game da yadda ake samun ƙaruwar wannan garkuwa da mutane a faɗin ƙasar. Yanzu gaskiya wasu na faruwa, mun ga abin da ya faru a Kaduna, a Borno, sannan a Sakkwato.

“Tabbas, gwamnati na sa ido sosai da hakan ba wai kawai ta sa ido ba, har ma da tabbatar da cewa jami’an tsaro na ɗaukar matakan da suka dace don ganin an dakatar da hakan sosai.

“Yanzu kamar yadda na faɗa, Shugaban Ƙasa ya ce wannan lamari ne da ba za a amince da shi ba, kuma gwamnati ba za ta amince da sace-sacen mutane ko sace-sacen jama’a ko duk wani nau’i na laifi a wannan hanya ba.

“Muna ganin hakan yana faruwa kuma gwamnati na ɗaukar matakai masu inganci, da farko don daƙile hakan, da kuma dakatar da yaɗuwar wannan a fili.

“Muna ganin yadda jami’an tsaro su ma suke kai wa waɗannan hare-hare ko masu aikata laifuka, sai a ɗara matsa musu su ma su samu wasu munanan hare-hare. Amma gwamnati ba ta ɗaukar wani uzuri.

“Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin cewa dole ne hukumomin tsaro cikin gaggawa su tabbatar da cewa waɗannan yara da duk waɗanda aka yi garkuwa da su.”

By Editor