’Yar’Adua ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dokokin Nijeriya, Abdulaziz Musa Yar’Adua, ya zama sabon Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa.

An naɗa ’Yar’Adua, ɗan majalisa na jam’iyyar APC, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar kwanaki biyu bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi.

Ningi, mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, ya zargi babban zauren majalisar da karkatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 har na naira tiriliyan 3.7.

Duk da cewa batun ƙara kasafin kuɗi ba sabon abu ba ne a Nijeriya, amma wannan ne karon farko da wani ɗan majalisar dattawa da ya taka rawar gani wajen zartar da kasafin ya zargi ’yan majalisar da irin wannan aiki.

A ranar Talata, Ningi ya ɗora laifin murabus ɗin nasa a kan abubuwan da suka faru a Majalisar Dokoki ta ƙasa, da Arewa da ma ƙasa bakiɗaya.

Ƙungiyar ta kuma bayyana Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa a matsayin mai magana da yawunta domin maye gurbin Sanata Sumaila Kawu wanda majalisar dattawa ta gargaɗi ya daina raba muqamai da za su iya haifar da tarzoma a ƙasar.