An dakatar da ’yan wasan Kamaru 62 saboda zaftare shekaru

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kamaru ta dakatar da ‘yan wasan ƙasar 62 bisa laifin coge wajen bayyana shekaru, cikinsu har da matashi mafi ƙarancin shekaru a tawagar da ta buga gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a watan Janairu.

Hukumar ta FECAFOOT ta fitar da jerin sunayen a hukumance a ƙarshen wannan makon, ciki harda Wilfried Nathan Douala mai shekaru 17 wanda ya ba da mamaki cikin tawagar Rigobert Song a gasar da aka kammala a Ivory Coast.

A cewar FECAFOOT, mai tsaron ragar Victoria United ya yi ƙarya game da shekarunsa, don haka an hana ɗan wasan shiga wasannin share fage na Elite League.

Ba a bayyana ainihin shekarun Douala ba, amma lamarin haɗa da wasu ‘yan wasa 61 da aka dakatar saboda ƙin bayyana shekarun su na asali.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin hukumar FECAFOOT ƙarƙashin jagorancin Samuel Eto’o ke da nufin rage matsalolin gudanarwa da aka fuskanta a baya a lokacin da kuma bayan kammala kakar wasan ƙwallon ƙafa ta Kamaru.