An karrama marubuci Abba Abubakar Yakubu

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Fitaccen marubucin nan kuma jarumin finafinan Kannywood, Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ya taɓa faɗa cewa, ‘Duk wani abu mai kyau da ka ke yi duniya tana gani, kuma wata rana za ka samu sakamakonsa.’

Wannan bayani nasa ne ya fito a fili jama’a suka shaida, a ƙarshen makon da ya gabata, inda wata cibiya mai koyar da ilimin fasahar sadarwa da kula da adana littattafai, wato Information and Library Science, mai suna Majema College of Advanced Studies Jos ta karrama marubuci kuma ɗan jarida, Abba Abubakar Yakubu, sakamakon jajircewa da gudunmawar da yake bayarwa a harkar rubutu da ilimantarwa.

A cewar shugaban cibiyar Ambasada Ghali Musa Abba, sun karrama Abba Abubakar Yakubu ne wanda ya kasance haziƙin marubuci, masanin zamantakewar al’umma, da ke ba da gudunmawa wajen tarbiyyar matasan marubuta, da koyar da ɗalibai hanyoyin inganta karatunsu, da yadda za su yi fice a duk wani fanni na rayuwa da suke sha’awar bunƙasa iliminsu a kai.

Ya ce, sun daɗe suna nazari da ayyukan marubucin wanda yake yi a matsayinsa na ɗan jarida kuma malamin makaranta, a kafafen sadarwa daban-daban, ciki har da jaridar Blueprint Manhaja, inda yake gabatar da shafin ‘Aiki Da Hankali’ a kowanne mako don faɗakar da jama’a game da harkokin siyasa da zamantakewa, da kuma hira da yake yi da marubutan adabi, ko kuma sharhi kan harkokin rubuce-rubucen Hausa.

A jawabinsa na godiya Malam Abba Abubakar Yakubu ya yabawa shugabannin wannan cibiya ta Majema College of Advanced Studies bisa karramawar da suka yi masa, duk da kasaancewar akwai wasu da suka fi shi cancanta, amma suka ga shi ne ya dace su karrama.

Ya ƙara da cewa, babu shakka wannan karramawa da aka yi masa ta ƙara masa ƙaimi wajen cigaba da ayyukan da ya saba don tallafawa ayyukan marubuta da wallafa domin yaɗa ilimi da ƙarfafa gwiwar sauran marubuta.

Yana mai cewa wannan karramawa ita ce abin da ya fi faranta masa rai, kasancewar an ba shi ne game da harkar rubutu da ilimantarwa, abubuwan da wasu ba sa ɗauka da muhimmanci.

Ya yi fatan sauran cibiyoyin ilimi za su riqa jawo marubuta a jiki da ba su damar yadda za su taimaka musu da baiwar da suke da ita don cigaban makarantunsu da abubuwan da suka sa a gaba na ilimi, saboda a cewarsa marubuta mutane ne masu baiwa ta musamman.