Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince kan a biya ma’aikatan jihar kuɗin hutu domin ba su damar yin walwala a cikin watan Ramadan.
Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce tuni ma’aikatan jihar suka fara samun biya a Larabar wannan makon.
Sanarwar manema labarai da Sulaiman ya fitar ta ce, kuɗin hutun kashi 10 cikin 100 ne na albashin da ma’aikaci ke ɗauka a shekara.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tun bayan da Lawal ya karɓi ragamar mulkin jihar, gwamnatinsa ta ɗauki lamarin walwalar ma’aikatan jihar da wasa ba.
Don kuwa, “Ya biya bashin albashin da ke kan gwamnatin da ta gabata, ya biya giraduti, sannan ya amince da ma’aikata su riƙa samun albashi na wata 13.
“Duba da yanayin matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a ƙasa, Gwamna Lawal ya yanke shawarar ya kyautata wa ma’aikata da masu riƙe da muƙaman siyasa ta hanyar biyan su kuɗin hutu,” in ji sanarwar.
