Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ana gudanar da bikin Ranar Marubuta ta Duniya ne a ranar 3 ga watan Maris na kowacce shekara, domin ƙara zaburar da marubuta a ko’ina a duniya game da gudunmawar da suke bayarwa wajen faɗakarwa da ilimantar da jama’a da suke yi, musamman matasa da ɗaliban ilimi. Tun a shekarar 1986 aka fara bikin ranar a faɗin duniya, bayan shawarwarin da ƙungiyoyin marubuta da mawaqƙa daban-daban suka riƙa bayarwa don ganin an ware wata rana guda da za a riƙa tattauna abubuwan da suka shafi harkar rubutu da basirar ƙirƙira.
Sau da dama jama’a sun fi mayar da hankali ne ga littafi ko labarin da marubuci ya wallafa ba tare da tunanin ƙalubalen da shi marubucin ya fuskanta kafin ya kai ga wallafa littafinsa ba. A irin wannan rana ƙungiyoyin marubuta da dama kan shirya taruka ko shirye-shirye a rediyo da talabijin ko cikin jaridu domin bayyana faɗi tashin da marubuta ke fuskanta, kafin su kai ga iya rubuta littafinsu na farko, ko kafin su samu karvuwa a wajen masu karatu, da kuma ƙalubalen da suke fuskanta a cikin al’umma, musamman daga iyaye ko iyalinsu. Sannan har-wa-yau akwai ƙalubalen satar fasaha daga malalatan marubuta ko masu amfani da rubutun wasu suna shirya finafinai ko sanyawa a YouTube ba tare da izini ba, suna ci da gumin wasu.
Sai dai a yayin da marubuta a wasu ƙasashen duniya suka raya bikin ranar da taruka da rubuce-rubuce, a nan Nijeriya qalilan daga marubuta ne suka ma san akwai wata rana irin haka, ballantana har su shirya wani taro ko rubutu game da hakan. Aisha Abdullahi Yabo ɗaya daga cikin marubutan Hausa wacce ta rubuta littafin, ‘Fargar Jaji’ ta ce ita sam ba ta da labarin akwai wata rana irin wannan, amma kuma ta yi farinciki da samar da rana ta musamman don tattauna muhimmancin rubutu da gudunmawar marubuta a duniya.
Ita ma marubuciya Jamila Umar Tanko wacce ta yi littafin ‘Hira Da Matattu’ ba ta san da akwai wata rana da aka ware don girmama ƙoƙarin marubuta ba. Amma ta ce, samar da wannan muhimmiyar rana yana nufin duniya ta fahimci gudunmawar marubuta da tasirinsu a cikin al’umma, savanin a baya. “Domin ko fim ake kallo mantawa ake yi da akwai wanda ya rubuta, mutane sun fi mayar da hankali wajen yabawa jaruman da suka fito a cikin fim ɗin,” a cewarta.
A wajen marubuciya Hajara Ahmad Oum-Nass, wacce ta rubuta littafin ‘Jini Ya Tsaga’ tsayar da Ranar Marubuta ta Duniya ba ƙaramin farinciki ya sa ta ba. Har ma tana cewa, ‘Hakan ya ƙara tabbatar min da rubutu ba abin banza ba ne ko kuma rashin aikin yi, kamar yadda wasu mutane suke tunani. “Da iya wannan ranar kaɗai ta isa na kusa da kai ya yi alfahari har ya bayar da labarin ɗan uwansa ma marubuci ne!” Malaminta Jibrin Adamu Jibrin Rano, marubucin littafin ‘Dama Sun Faɗa Min’ shi ma ra’ayinsa kenan, inda ya ke cewa, “Abin daɗi ne sosai a ce marubuci ma yana da wata rana ta musamman da aka ware don jinjina masa.”
Laila Abdullahi marubuciyar littafin ‘Guguwar Fansa’ cewa ta yi, “Sosai nake jin farinciki idan na tuna marubuta suna da rana ta musamman da aka ware domin su, duk da marubuta sun cancanci fiye da haka ma, ko mako guda aka ware don karrama marubuta ba a faɗi ba. Ina alfahari da kasancewata marubuciya, ina roɗon Allah ya ƙara ɗaukaka rubutu da marubuta gabaɗaya.”
Sai dai duk da haka wanne ƙalubale ne za a iya cewa marubuta a wannan zamani ya kamata su fi mayar da hankali a kansa? Ta yaya marubuta za su canza akalar tafiyar da harkokinsu na rubutu?
Sadiya Garba Yakasai na daga cikin fitattun marubutan Hausa masu talifi, wacce ta rubuta littafin ‘Marayu Ma ‘Ya’ya Ne’, a ra’ayinta, “Ya kamata marubuta su dage a fannin bincike da cika ƙa’idojin rubutu, sannan su tantance irin rubutun da za su riƙa yi. Yanzu ba jigon soyayya ko zaman aure ne ke jan hankalin masu karatu ba, akwai abubuwa da dama da suka addabi al’umma kuma da yawan mutane ba su da sani a kai. Idan ana tavo irin tsaurin rayuwar da ake fuskanta a yanzu, rashin tarbiyya da rashin sanin girmama shugabanni da sauran su. Har-wa-yau da ma yadda su kansu shugabannin suka yi wasarairai da nauyin al’ummar su to, lallai za a samu cigaba.”
Wannan ra’ ayi nata ya so ya yi daidai da na marubuciyar littafin ‘Zaƙi da Maɗaci’ Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, wacce take ganin abin da ya kamata marubuta su fi mayar da hankali a kai a wannan lokaci bai wuce, batun tsadar rayuwa, tarbiyya, ilimi, da sana’a ba. Domin a cewarta, “Idan muka dubi halin da ake ciki na tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tarbiyya, duk al’ummarmu na fuskantar waɗannan abubuwa ne a halin yanzu.
“Idan marubuta suka jajirce sosai wajen wayar da kan mutane akan waɗannan batutuwa, ina kyautata zaton idan jama’a suka gane suka sauya halayensu marasa kyau kuma suka ilimantu tare da aiki da ilimin, babu shakka za a samu waraka, musamman matasa da masu tasowa manyan gobe, kasancewar su ne ƙashin bayan rayuwar al’umma kuma shuwagabannin gobe masu fitowa daga cikin al’ummar da suke cikinta.”
Marubucin littafin ‘Ya’yanmu, Kabir Yusuf Fagge wanda aka fi sani da Anka cewa yake yi, akwai abubuwa da yawa da a yanzu suke damun al’umma a qasar nan da ya kamata marubuta su mayar da akalar rubuce-rubucensu a kai, kamar abin da ya shafi cin hanci da rashawa, tsaro, rashin tabbas na rayuwa, rashin iya jagoranci ko shugabanci, lalaci, rashin sanin kai, tarihi da sauransu. Ra’ayin da ya samu goyon bayan marubuci Abdullahi Hassan Yarima, wanda ya rubuta littafin ‘Ƙuncin Rayuwa’ inda ya bayyana marubuci a matsayin mutum ne da ke kallon matsalolin da ke damun al’umma ya yi rubutu a kai don ganin an fitar da A’i daga rogo, ko kuma an fitar da baki daga duma.
Akwai matsalolin da duk duniya ta shafa kamar matsalar rashin aikin yi da gurɓacewar tarbiyyar matasa da irin matsalar shaye-shaye da tashe tashen hankula a nan da can. Akwai babbar matsalar da marubuta tatsuniyar kimiyya (Science fiction) suka fi mayar da hankali a kai; wato irin ƙalubalen da ke fuskantar duniya na cigaba da kuma hatsarin da ƙirƙirarriyar fasaha ta ‘Artificial Intelligence’ ke tattare da ita. Akwai kuma matsala ta ɗumamar yanayi da ƙarancin abinci da kuma yawan al’umma da sauran su. Sannan akwai matsalolin da kowacce al’umma ke fama da irin nata. A ɓangaren mu akwai matsalar barace-barace da matsalar mace-macen aure, aikatau da sauran su.
Ya cigaba da cewa, “Yana da kyau marubuta su fi mayar da hankali kan matsalolin da ke daf da su da kuma hanyoyin da za a bi don magance su. Wani sa’in kuma marubuci zai iya farawa da ƙaramar matsala sannan ya gangara zuwa kan babba. Wani kuma zai iya kallon matsalar da gabaɗaya al’ummar duniya ke fuskanta. Sai dai ba koyaushe marubuci ke iya zuwa da gamsasshiyar amsa ba. Zai iya haska matsalar wasu su shiga su warware.”
Ana samun marubuta da dama da ke da irin wannan ra’ayin na kallon wata matsala a cikin al’umma su yi rubutu a kai da nufin kawo gyara. Daga cikin su akwai marubuciya Hauwa Shehu da ta rubuta littafin ‘Harin Gajimare’ wanda a ciki ta ilimantar da jama’a yadda varayin yanar gizo ke amfani da wasu dabaru suna cutar da jama’a wajen satar wasu muhimman bayanai daga wayoyinsu ko na’urorinsu na tafi-da-gidanka. Wani vangare da ba kasafai marubutan Hausa ke waiwaya ba.
A cewar marubuciyar, ‘l”Abin da ya ja hankalina wajen ɗaukar jigon shi ne yawaitar matsalolin damfara da satar bayanan da ake yi ta yanar gizo, wanda hakan babbar barazana ce ga duk wani mai amfani da na’ura, walau kwamfuta ko wayar hannu. Wannan dalilin ne ya sa na ga dacewar ba da tawa gudummawar wajen wayar da kan al’umma su fahimci girman matsalar da hanyoyin kauce mata.”
Ita ma tana ganin yin rubutu game halin da rayuwa ke ciki yana da muhimmanci, don a cewarta, “Shi rubutu a kodayaushe rayayye ne, haka kowanne zamani yana zuwa da na shi ƙalubalen. Saboda haka ya kamata marubuta su fi mayar da hankali ga abubuwan da suke da nasaba da yadda zamani da kuma yanayin da ake ciki.
Misali, a wannan lokacin akwai matsalar matsin tattalin arziƙi, rashin tsaro, da kuma sauyi na abin da ya shafi fasaha.”
Sadiya Ka’oje marubuciya ce da ta rubuta littafin ‘Jini Ɗaya’ ta ce akwai buƙatar marubuta na yanzu su karkata alƙalaminsu wajen yin rubutun da zai kawo gyara a rayuwar al’umma, kamar matsalolin zamantakewa irin rashin ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai, talauci da illar zinace-zinace da rage mudu. Ta ce, “Marubuci mutum ne wanda tunaninsa yake daban, zai iya lanƙwasa waɗannan matsaloli ya sanya su a cikin rubutu ta yadda al’umma za su fahimta, kuma ya amfane su.”
Ko ita ma Hajara Oum-Nass tana kallon marubuci a matsayin ɗan baiwa, wanda ke da basira da hikimar da zai iya sauya tunanin mutane, har ya iya fidda mutum a matsala kuma ya ilimintar da mutane ba tare da sun sani ba.
Hadiza D. Auta marubuciyar littafin ‘Zubar Hawaye’ a nata ɓangaren tana rubutu ne a duk lokacin da ta samu wani jigon da take ganin in ta yi rubutu a kai jama’a da dama za su amfana, domin kaucewa matsalar da ke damun al’umma da kuma kawo gyara a kan abubuwan da za su kawo ga bin hanyar gaskiya ɗoɗar.
Shi kuwa marubuci Jibrin Adamu Jibrin Rano hankalinsa ya fi karkata ne kan yadda littattafan marubutan yanzu suke saurin vacewa saɓanin na marubutan baya, duk kuwa da kasancewar a marubutan zamani ma ana samun haziqan marubuta na gani na faɗa. A nazarin da ya yi ya gano akwai buqatar samo amsoshin waɗansu tambayoyi, “Shin ko me ya sa marubutanmu na yanzu tun suna raye ake mantawa da rubutunsu, amma kuma marubutan baya ko sun mutu hakan ba ya hana a tuna rubutunsu har fiye ma da na waɗanda suke rayen? Shin me ya sa a zamanin baya ko marubuci bai yi suna ba ake karanta labaransa, amma kuma manazartan yanzu suke yin zaɓen wanda za su karanta rubutunsa, ta yadda ba sa karanta rubutun marubuci sai fitacce?”
Waɗannan su ne manyan ƙalubale biyu da suka fi tsayawa marubucin a maƙoshi, wanda kuma yana ganin su ya kamata marubuta su tsaya a nemo bakin zare.
Marubutan sun bayar da wasu shawarwari kan yadda za a gudu tare a tsira tare, kuma a inganta harkokin rubutun adabi. Hajara Ahmad Oum-Nass cewa take yi. “Abin da ya kamata marubuta su mayar da hankali a yanzu shi ne, dagewa da kuma ƙarfafawa junansu gwiwa. Kar su tava tunanin cewar ba za su iya ba, ko sun yi ba su dace ba, ko kuma su yi rubutu domin su samu suna. Shi aiki tuƙuru da tsaftacce alƙalami yana sa mutum ya kai matakin da bai taɓa tunanin zai taka ba a rayuwa.”
Ita ma Ruƙayya Ibrahim Lawal marubuciyar littafin ‘Wata Duniya’ shawara ta bayar tana mai cewa, “Ƙalubalen da ya kamata marubuta su mayar da hankali a kan rubuce-rubucensu shi ne inganta rubutunsu ta hanyar gamsasshen bincike. Su nutsu su bibiyi darussan rubutu da ake gudanarwa sannan su kaucewa satar fasaha, maimaita salon wani ko zuba shirmen abin da ba zai taɓa yiwuwa ba a labari ba.”
Laila Abdullahi cewa take yi, “Marubuta suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa a wannan halin da ake ciki, suna da hanyoyi masu yawan gaske waɗanda za su iya janyo hankalin masu ruwa da tsaki akan al’ammuran ƙasar nan. Allah Ya ba su baiwar iya canja goben ƙasa marar kyau don ya dawo mai kyau.”
