Tsaro: Lawal ya rattaɓa hannu kan wasu sabbin dokoki

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki da suka haɗa da doka haramta amfani da gilashin mota mai duhu da sayar da burodi mara ɗauke da shaida.

Sauran hanin sun haɗa da ɗura burodi a buhu da kuma saida fetur sama da lita 50 a lokaci guda ga abubuwan hawa.

A ranar Talata Gwamna Lawal ya sanya wa dokokon hannu don su fara aiki a jihar.

Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce doka mai lamba 02 da mai lamba 04, 2024, za su taimaka wajen daƙile abubuwan da suke haifar fa matsalar tsaro a jihar.

Ya ce an ɗauki wannan mataki ne biyo bayan wasu hare-haren ta’addancin da aka kai a wasu sassan jihar.

Sanarwar ta ce, “Biyo bayan hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a wasu yankunan ƙananan hukumomin jihar, musamman Zurmi, Shinkafi, Kaura Namoda, da Talata Mafara, da kuma sake dawowar ayyukan ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane a wasu sassa a jihar.

“Gwamna Lawalya sanya wa doka mai lamba 02, 2024 kan haramcin sayar da burodi mara ɗauke da shaida, saida burodi a buhu da sauran haramtattun ayyuka.

“Wajibi ne gidajen gasa burodi su sanya wa burodin shaidar masana’antarsu da cikakken da sauran bayanai.

“Ba a yarje wa ɗaukacin gidajen mai su sayar wa abin hawa fetur sama da lita 50 a lokaci guda ba. Kuma gidajen mai za su riƙa aiki ne daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

“A tsakanin hedikwatar ƙananan hukumomi kaɗai aka yarda a sayar a kai ko sayar da burodi. Amma a cikin Gusau dokar ta taƙaita ne a yankunan hanyar Damba—Zaria, hanyar Gada Biyu—Sokoto, Command Guest House da ke hanyar Kaura Namoda, da kuma hanyar Gusau Garage—Dansadau,” in ji sanarwar.

Bugu da ƙari, Gwamna ya sanya wa doka mai lamba, 04, 2024 don haramta amfani da gilashin mota mai duhu a Zamfara.

A cewafmr sanarwar: “An haramta wa masu abubuwan hawa rufe lambobin motocinsu yayin da suke tuƙi.

“Dole ne ga masu abunuwan hawa su mallaki muhimman takardu da kuma kiyaye dokaramfani da hanya ta Jihar Zamfara mai lamba 2, 2015 ko makamancinta.”