Ba dalilin da zai sa ka ƙaro aure alhali gidanka bai ƙoshi ba – Nafisa Usman

“idan ba ki da haƙuri ba za ki iya samun kwangila a gwamnati ba”

Daga AISHA ASAS

Mace halitta ce da aka halita da wata baiwa ta musamman da ba kasafai ake samunta a maza ba, wato baiwar iya yin ababe da dama a lokaci guda. Ma’ana dai mace za ta iya aikin kula da kanta, iyalinta kuma ta samu iya neman kai ba tare da ɗaya ya samu rauni ba. Haka kuma mace za ta iya yin ayyuka da dama da ake ganin ƙarfin ƙwaƙwalwarta da ƙwazonta bai kai ba.

A wannan makon shafin Gimbiya ya ɗauko maku matar da za ta tabatar da batun da muka yi a sama, jajirtaciyyar mace mai kamar maza da ta cancanci mu kira ta da gimbiya mai haskawa mata hanya.

A tattaunawar, za ku ji yadda ta zavi ɗaya daga cikin ayyukan da aka fi alaƙanta su da maza, da kuma yadda hakan bai sare mata gwiwa ba wurin ganin burinta ya cika ba. Don haka idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Hajiya Nafisa Usman:

MANHAJA: Wacce ce baƙuwar tamu ta wannan makon?

HAJIYA NAFISA: Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Nafisa Usman. Haifaffiyar Jihar Sakkwato, kuma a Sakkwaton na taso, don haka dukka karatuna a nan na yi shi. Baya ga haka, na yi aure a nan Sakkwato.

Ni matar aure ce, kuma uwa, domin alhamdu lillah, Allah Ya azurta ni da samun yara uku. ‘Yar kasuwa da take harkar kwangila. Wannan a taƙaice kenan.

Kasancewar kwangila ta karkasu da yawa. Wane vangare ki ka fi mayar da hankali kansa?

Ɓangarena na gine-gine ne da kuma ƙawata gida, wato ‘interior decoration’ a turance.

Ko me ya sa ki ka zaɓi ɓangaren sana’ar yin kwangila?

To, kasancewa ta mace mai son saka kanta ababe mabambanta, waɗanda za su sa hannuna cika, wato ban cika son zama ba na yin komai ba. Baya ga haka, Ina matuƙar son harkar gine-gine. Wannan dai a taƙaice shi ne dalilin nawa.

Sau da yawa ana keve wasu ayyuka da ake wa kallon ba su dace da mace ba, musamman ma a nan Arewacin Nijeriya. Shin a matsayinki ta mace ‘yar Arewa ko kin fuskanci wani ƙalubale a harkan kwangila, duba da cewa tana daga cikin ayyukan da ake yi wa kallon na maza?

Wannan gaskiya ne, kuma zan iya cewa tabbas na fuskanci irin wannan matsala, musamman ma kasancear maza sun fi yawaita a harkar, sai kiga suna yi min kallon ba zan iya ba. Ba zan bada abinda ake buƙata ba. Amma dai hakan bai sare min gwiwa ba, asalima yakan ƙarfafa ni, in saka Allah a gaba, in kuma yi iya yina, kuma cikin ikon Allah sai kiga kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Wasu mata da suke yin irin sana’ar da ki ke yi, na ƙorafin ba a cika ba wa mata kwangila, wato dai ba a cika yarda da za su iya ba. Ko a naki ɓangaren kina cin karo da abinda ya yi kama da hakan?

Ni dai a ɓangarena gaskiya ba zan ce na taɓa cin karo da wani abu makamancin haka ba, kawai dai ni abinda na yarda da shi, idan ka sa Allah gaba, da kuma yadda za ka tunkari abin, to tabbas za ka samu. Don haka ni ban fuskanci wannan ƙalubale ba.

A kwanakin baya wani ya zargi gwamnatin Jihar Sakkwato da cewa, ba ta ba wa ‘yan kwangilar da suke nema aiki, sai dai su bayar ga kawunansu. A matsayinki ta wadda ta zama ‘yar gida a harkar kwangila, me za ki iya cewa dangane da wannan zargin?

To, magana ta gaskiya ana bayarwa, amma kuma magana ce ta ‘wa ka sani’, saboda ba qaramin aiki ba ne samun kwangila. Hanyoyin ma da za ka bi idan ba ka da haquri ma ba za ka iya ba. Don haka ma wani wurin ba za ka iya kai wa ba tare da sanin wani a gwamnati ba.

Idan ka wanke jiki kawai ka ce a matsayinka na ɗan kwangila kana son samun kwangila don ka cancanta, hanyoyin da za ka bi don isa ga kwangilar a tsarin nata ma kawai za ka sha wahala, amma idan ka san wani zai zo ma da sauƙi.

A rayuwa bakiɗayan ta kowa na da irin nasa tsarin, wanda zai iya bambanta da na wani. A sha’anin sana’ar taki ta kwangila, waɗanne irin hanyoyi ko tsari ne ki ke da shi da ki ke bi don ganin kin samar da ingantacciyar kwangila da za a yaba?

To ita sha’ani ta kwangila dama idan aka ba ka ita abinda ake so aiki da cikawa, abinda ake buqata ka tabbatar da ka yi shi yadda ake so. Masu iya magana sun ce ‘don tuwon gobe ake wanke tukunya’ ko. Idan ka yi aiki tsakani da Allah, to za ka samu abinda ka ke so, domin wanda ka yi wa zai ji daɗi, kuma zai sake neman ka.

Amma idan ka sa cuta, ko ka samu yau, to fa ka jira gobe ba za ka samu ba.

Idan za a fitar da kwangila a Jihar Sakkwato, ko akwai wata hanya da ake bi wurin sanar da masu buƙata su zo su nema, kamar ta saka wa a jaridu haka, yadda wasu wuraren ke yi?

Ni dai gaskiya ban tava cin karo da irin haka ba, duk da ba zan ce ba a tava yi ba, sai dai a shekarun gwagwarmayar aikin kwangila da na yi ban tava gani ba, ko jin labari ba.

A matsayinki ta mace mai fafutukar neman na kanta, wane irin kira za ki yi ga matan da ke zaman kashe wando?

To a gaskiya a wannan yanayi da muke ciki yanzu ya kamata a ce mata sun kama sana’a komai ƙanƙantar ta. Ba wai ina magana ne kan matan aure kawai ba, har matan da suke gida. Ita sana’a dai taimakon kai ce, don haka wadda ba ta da aure tana yi ne don ta taimaki kanta don gudun ta bi wata hanya marar kyau, wadda ke da aure kuwa za ta tallafa wa mijinta da ɗan inda aka gaza.

Wannan yanayi da ake ciki ba za ki dogara ga wani ya ɗauke lalurorinki dukka ba, gwara ki tashi ki nemi naki, don shi ne kawai mafita a halin da muke ciki a yanzu.

Menene sirrin ɗaukakarki?

Allah! Addu’a. idan ka zauna, ka kashe dare ka neme Shi, zai amsa ma, kuma ba abinda ba za ka samu ba.

A wannan yanayi da muke ciki na matsin rayuwa, ma’aurata da yawa sukan samu yawaitar hatsaniya, har wani lokaci a kai ga rabuwar aure, sakamakon rayuwar ta yi tsanani, kuma wasu matan ba su fahimta, su kuma mazan fushin da suke da shi ga hauhawan faraci sukan sauke shi ne a gida, ta hanyar yawan faɗa da sauransu. A matsayinki ta matar aure, wacce hanya ki ke ganin ya kamata mata su bi wurin ganin nasu aure ya tsira daga irin wannan matsala?

Na ɗaya mata su qara haƙuri, kuma su yi ƙoƙarin ganin sun karvi halin da ake ci a kula da gida. Yadda yanayin rayuwar ta zo ki amshe ta a haka. Idan kin saba kashe 2,000 a rana, ki koma kina maneji da 1,000, to ki yi haquri tare da yin dubarun da za ta samar da yadda za a iya ɗan rufawa kai asiri.

Idan ba ki aikin komai, to duk yadda za a yi ki lalava maigidanki, ko idan akwai inda za a taimaka miki, ki samu sana’ar da za ki yi koda cikin gida ne. idan kin samu, ko ba da sanin maigida ba ki dinga taimaka wa a lalurorin gida. Idan kina ɗauke wasu laluran komai zafin zuciyar da ya zo da ita, zai sauko, domin namiji ne, kuma namiji bai son bani-bani.

Ke ma sai ki sauko ki daidaita buqatunki, abinda ya ba ki, ki yi haƙuri da shi, idan kina da sana’a, sai ki ƙara zuwa ga yadda zai maki daidai. Idan ba ki da ita kuma, sai ki ƙara haƙuri.

To a wani ɓangaren kuma, za ki samu wasu mazan da ba su iya riƙe gidansu ba, ba wai don ƙeta ba, sai don ƙarfin su bai kai na ba su dukka buƙatu na ci da sha ba, amma a cikin irin wannan yanayi sai kiga da wasu mazan sun samu hali, wataƙila wani can zai hango wahalar da iyalansa ke ciki ya ɗauko wasu ‘yan kuɗaɗe ya ba shi don ya ƙara jari, amma sai ya buge da ƙaro auren da kuɗin.

To a gaskiya wannan ba daidai ba ne, idan har ba ka iya ba wa iyalanka buƙatun da suka zama dole, to auren bai da amfani gaskiya. Banga dalilin da zai sa ka ƙaro aure ba alhali gidanka bai ƙoshi ba, kaga kenan ka ƙara nauyi kan nauyi kenan.

Kuma wani abu da mazan ba su gane ba shi ne, ba su da masaniyar wadda za su kawo ɗin za ta iya haquri ko ba za ta iya yi kamar yadda ta farkon ta yi ba. Gara a ce ka daidaita gidanka tukuna, ya zama idan har za ka ƙara auren ka tabbatar kana da abinda za ka iya ciyar da su dukka.

Su kuɗi kamar ashana suke idan ba a juya su, ka zo ka yi aure, wataƙila ka ji daɗi na watanni uku, kuɗi sun zo sun ƙare, sai fitina ta biyo baya, daga nan sai matsala, kafin ka ce me sai a ji saki.

Daga ƙarshe wane kira za ki yi ga ‘yan uwanki mata da suke sana’ar kwangila?

Kirana gare su shi ne, su yi haƙuri da duk yadda kwangilar ta zo masu, kada su sa dogon buri ciki, kuma a yi ta tsakani da Allah, kuma kada su yi dubin cewa, “ƙawata tana yin kwangila manya ta fi ni samu,” abinda duk Allah Ya ba ki ki amsa da godiya ki yi amfani da shi. Ki daina hangen inda ba ki kai ba. Ki yi shi tsakani da Allah. Gobe idan Allah Ya so, sai ya ba ki wadda ta fi ta. Kuma haƙuri na da kyau, domin kamar yadda na ce, a baya, idan ba ki da haƙuri ba za ki samu ba.

Mun gode da lokacin ki.

Yawwa, ni ma na gode.