Da Ɗumi-ɗumi: Nijeriya ta buɗe iyakokinta da Nijar

*Ta janye mata ragowar takunkumai

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin gaggawa kan sake buɗe iyakokin Nijeriya da Nijar ta ƙasa da sama, tare da ɗage sauran takunkuman da aka ƙaƙaba wa ƙasar.

Mai magana da yawun Shugaba Ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce hakan ya yi daidai da umarnin ECOWAS wanda ta bayar yayin taron da ta yi ranar 24 ga Fabrairu a Abuja.

A cewar sanarwar, “Shugabanni ECOWAS sun amince a kan janye takunkuman da aka kafa wa Jamhuriyyar Nijar, Mali, Burkina Faso da kuma Guinea.

“Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin ɗage waɗannan jerin takunkuman da aka kafa wa Nijar nan take:

(1) Rufe iyaka Nijeriya da Nijar, ƙasa da sararin samaniya, da hana jiragen sama zirga-zirga wajen shiga da fita ƙasar Nijar.

(2) Dakatar da kowane nau’i na hada-hadar kuɗi tsakanin Nijeriya da Nijar, da sauran hada-hada ciki har da bai Nijar wutar lantarki.

(3) Riƙe kadarorin da Nijar ke su a Babban Bankin ECOWAS da sauran bankunan kasuwanci.”

Nijar ta fuskanci takunkumi daga ECOWAS ne tun bayan da sojojin ƙasar suka kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum.