Yadda za mu dawo da ɗabi’ar karatun littafi

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata ne, na samu gayyata daga wata cibiya mai kula da ilimin matasa a fannonin ilimi daban-daban a matakin gaba da sakandire, mai suna Majema College of Advanced Studies Jos, wacce ta karrama ni daga cikin jerin mutanen da ta zaɓa don yabawa ƙoƙarin da suke yi wajen ba da gudunmawa a harkokin ilimi da rayuwa.

Wannan karramawa da na samu a cikin jerin manyan mutanen da aka zaɓo daga ɓangaren malaman addini da na boko, ’yan kasuwa, ‘yan siyasa da kuma ’yan jarida, ta yi matuƙar birgeni, musamman ganin cewa an ba ni shaidar karramawar ne a saboda dalilan da masu makarantar suka bayyana, wato gudunmawata a harkar rubuce-rubuce da aikin jarida. Wannan abu ne da ya yi matuƙar faranta min rai, bisa la’akari da cewa duk abin da ka ke yi wasu na kula da shi.

Amma ba wannan ne ya fi faranta min rai ba. Abin da na fi jin daɗi a kai shi ne yadda shugaban makarantar Ambasada Ghali Musa Abba ya ɗauki nauyin ɗalibai marayu da ’ya’yan masu ƙaramin ƙarfi don tabbatar da ganin cewa maraici da rashin gatan da suke ciki bai hana su samun ilimi mai inganci ba.

Kuma wani abu da zai ƙara ƙayatar da kai, shi ne daga cikin waɗannan ɗalibai da ake tallafawa har da waɗanda ba musulmi ba. Duk kuwa da kasancewar wanda ya kafa makarantar Musulmi ne daga tsakiyar cikin garin Jos wanda ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

A tattaunawar da muka da shi, shugaban makarantar ya bayyana min cewa, kasantuwar ya taso a cikin unguwar talakawa wacce ake yi wa kallon matattarar taƙadaran yara, talauci da ƙazanta. Don haka ya yi tunanin me zai yi don ya ba da gudunmawar sa ta yadda zai ceto wasu daga cikin irin waɗannan matasa da ƙananan yara da ake yi wa kallon rashin gata ne yake sa su shiga hanyoyin da ba su kamata ba.

Bisa la’akari da yanayin taɓarɓarewar zamantakewar da ake fuskanta a Jos, na rashin ingantaccen tsaro da faɗace-faɗacen ƙabilanci. A tsakanin shekara 17 da ya yi yana tafiyar da wannan makaranta an samar da vangaren rainon yara, firamare, sakandire zuwa matakin gaba da sakandire. Kuma kamar yadda na bayyana a baya akasarin ’yan makarantar sun fito ne daga iyalai marasa ƙarfi.

Ya ƙara da cewa, ya ɗauki wannan hanya ne ta samar da ilimi saboda imanin da ya yi lallai ilimi ne yake canza rayuwar al’umma, daga mai koma-baya zuwa ga cigaba. ‘Na yarda sai da ilimi kowacce al’umma take samun bunqasa da cigaba. Kuma waɗannan ɗalibai ne nake sa ran watarana nan gaba za su kawo wannan canji da cigaban da muke burin gani.

Ban yarda cewa mutum ya mayar da hankali kan ’ya’yansa kaɗai ba, ya bar sauran yaran maqwaftaka cikin jahilci da rashin kyakkyawar makoma. Domin duk ilimin da yaranka za su samu, za su dawo su cigaba da rayuwa da waɗannan yaran da ka yi watsi da rayuwarsu. Ni ma nan gaba ban san waye zai riƙe min yarana ba, don haka nake ƙoƙarin ganin rayuwar waɗannan marayun yara ta inganta tare da nawa yaran.’

Kawo yanzu daga cikin abubuwan cigaba da wannan makaranta ta samu har da buɗe babban ɗakin karatu na laburare da aka samar masa da littattafai daban-daban, domin farfaɗo da ɗabi’ar son karatu a zukatan waɗannan ɗalibai, bisa tallafin wata cibiyar kula ilimi da adana littattafai mai suna Books2Africa, waɗanda suka taimaka wa makarantar da littattafai kimanin dubu 5 da ɗari 7, a fannonin ilimi daban-daban. Littattafan da aka kiyasta kuɗin su zai iya kai Miliyan 15, a cewar shugaban makarantar za su ƙara inganta ilimin da suke koyarwa a fannin fasahar sadarwa da adana bayanai, wanda a baya sai dai su yi amfani da Ɗakin Karatu na gwamnatin jiha, wajen koyar da ɗaliban.

Da nake jin ta bakin wakilin Cibiyar Books2Africa, Mista Gideon Maram, ya bayyana cewa sun ba da gudunmawar waɗannan littattafai ne kyauta, don ƙara ƙarfafa gwiwar makarantar, yadda za ta inganta ilimin da take samarwa ga ɗalibanta, saboda koma-baya da ake samu na ilimi a waɗannan yankuna na cikin garin Jos.

Ya yi nuni da cewa, ‘Idan ba a dawo da halayyar karatun littafi ba, nan gaba kaɗan jahilci zai sake mamaye al’umma. Domin kuwa duk abin da ka karanta daga littafi ba ya ɓacewa mutum da sauri, ba kamar wanda ya ji ko ya gani a waya kawai ba.’

Makarantar Majema College of Advanced Studies ta samar da wata dabara ta yadda za a tabbatar da ɗaliban suna shiga ɗakin karatun don buɗe littafi su yi nazari, aƙalla sau biyu a mako, inda ake ɗaukar sunan ɗaliban ta yadda zai shiga cikin makin da za a haɗa musu lokacin jarrabawa. Ko da kuwa a wanne matakin karatu, ɗalibi ya fito, an yi masa tsarin da zai samu awa biyu a ɗakin karatu.

Ummu-Salma Abubakar Tahir da Ummu-Kulsum Sa’id Usman, tsofaffin ɗalibai ne da suka yi karatu a fannin kula da ɗakin adana littattafai da bayanai, kuma yanzu haka suke aiki a wannan sabon ɗakin karatu da aka ƙaddamar, sun bayyana min cewa, duk da yake yanzu zamani ya zo da abubuwa na ɗauke hankalin ɗalibai daga karatun littafi, sun fi mayar da hankali a wayoyinsu na hannu da kallace-kallace, amma sanadiyyar buɗe irin waɗannan ɗakin karatu an fara jawo hankalinsu zuwa ga shiga ɗakin karatu suna zama su ɗauki littafi su karanta, ko da kuwa na awoyi ƙalilan ne.

A cewar Ummu-Salma, ‘Ɗalibai suna ƙoƙarin shiga su yi karatu ko da ma ba ranar karatunsu ba ne. Wasu ma daga maqwaftan anguwa suna shiga su yi karatu, duk da ba ɗaliban makarantar ba ne.’ A ƙarin bayanin da ta yi, Ummu-Kulsum ta bayyana cewa, ‘Ilimin da ake samu a karatun littafi ba a samu a waya, musamman karatun ilimi na makaranta. Tilas sai ɗalibi ya yi bincike a littafi sannan zai fahimci ilimin da ake koya masa.’

Wani marubuci da na haɗu da shi a wajen ƙaddamarwar mai suna Suleiman Isa Musa, wanda aka fi sani da Peace Jagaban, ya ce ya ji daɗi sosai da samar da wannan ɗakin karatu na al’umma da shugabannin makarantar suka yi, wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa kan fafutukar da suka daɗe suna yi ta dasawa matasa da yara masu tasowa kishin son yin karatu. Ya ce, ‘Duk al’ummar da take son ta cigaba tilas ta farfaɗo da ɗabi’ar son karatu a tsakanin al’ummarta, domin a littafi ake samun ilimi.’

Suleiman Jagaban shi ma ya yi alƙawarin ba da gudunmawar littafin da ya buga don ƙara zaburar da ɗalibai su yi karatu, mai suna ‘FOCUS’, ga ɗakin karatun wannan makaranta, domin ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Na ɗauki dogon lokaci ina wannan bayani ne domin fahimtar da mu muhimmancin sake waiwayar karatun littattafai na ilimi da na nishaɗi domin dawo da kimar littafi da rubuce-rubuce, wanda hakan yana da tasiri sosai ga cigaban harkokin ilimi a cikin al’umma. Sannan a samu wasu mutane da za su yi koyi da Ambasada Ghali Musa Abba, wanda ya sadaukar da duk abin da ya mallaka don ganin ya kafa wannan cibiyar ilimi, don ceto yara matasa maza da mata, daga faɗawa mummunan rayuwa, da ƙangarewa, zuwa ga wasu jakadun ƙwarai da al’umma za ta yi alfahari da su.

By Editor