Mulkin soja

Daga AMINA YUSUF ALI

Idan ka ji mutum yana fatan mulkin soja a Nijeriya, to cikin biyu ɗaya ne; ko dai yaro ɗan 90’s wanda bai san mene ne mulkin soja ba, ko kuma babban wanda bai san ciwon kansa ba.

Waɗannan su ne suke fatan sojoji su yi juyin mulkin a Nijeriya. Duk wanda ya san mulkin soja, to ba zai yi fatan sojoji su karvi ragamar ƙasar nan ba a halin da ake. Ko ni nan da aka haifa a zamanin mulkin Abacha, ruwan zafin da ake mini wanka da shi daban yake da na waɗanda da aka haifa a ƙarƙashin mulkin Demokraɗiyya. An ci baƙar wuya a mulkin Abacha ba kaɗan ba.

A mulkin soja babu faɗar gaskiya ko bayyana ra’ayi. Babu zanga-zanga in ba ta goyon bayansu ba; ba kowa ya isa ya yi magana ba. Idan kuma ka yi magana ta sava abin da suke so ko suke aikatawa za ka sha ɗauri, ko su kashe ka, ko a ɓatar da kai.

Daga cikin waɗanda suka sha ɗauri a mulkin soja akwai: Sule Lamido da Abubakar Rimi da Malam Ibrahim Zakzaky da Malam Gero Argugu da Moshood Abiola da Shehu Musa ‘Yar Adua. Akwai kuma irin su Wole Soyinka waɗanda sai guduwa suka yi suka bar ƙasar. An rataye Ken Saro-Wiwa, an ɓatar da ɗan jarida Dele Giwa ta hanyar aika masa wasiƙa mai ɗauke da bam a jiki wacce ta tarwatsa shi har lahira, da ire-iren waɗannan da dama.

Shehu Sani har litattafai ya rubuta a zaman da ya yi a gidan yari. Idan soja ya gawurta, sai ya haramta Fesbuk da Tuwita balle ku hau ku sanar da duniya hali da kuke ciki.

Fetur ɗin da muke siyan lita 700 zuwa 800 a yau, idan soja yaga dama sai ya mayar da shi 5,000 kuma babu yadda muka iya. Bayan haka, duk irin ayar da zai gasa mana, babu wanda ya san ran da zai sauƙa a kan mulki ballantana mu yi zaton zaɓe zai zo mu raɗa shi da ƙasa.

Duk lalacewar Demokraɗiyya tafi mulkin soja. Ko ba komai yau muna iya faɗan albarkacin bakinmu idan ta kama kuma mu murniƙe da zanga-zangar da dole sai gwamnati ta waiwaye mu ko da ba za ta biya mana buƙatunmu duka ba. Saɓanin mulkin soja da za a tarwatsa mu da ruwan zafi ko a buɗe mana wuta idan muka fita zanga-zanga.

Masu son sojoji su yi juyin mulki a Nijeriya don Allah ku yi haƙuri, ku daina mana fatan masifa; masifa a kwance take Allah Ya la’anci wanda ya tada da. Idan rayuwa a ƙarƙashin mulkin soja kuke so, ga ƙasar Burkina Faso ko Chadi ko Guinea ko Mali ko Sudan ko Nijar ko Gabon ku zaɓi wadda tayi muku kuje can. Amma mu ku bar mu da lalatacciyar Demokraɗiyyarmu.

Bari mu ɗan yi waiwaye adon tafiya kan bayanin da Malam Mahmud Jega ya yi mana a kan mulkin soja saboda ire-irena ‘yan ƙasa da shekaru 30 ba su san menene mulkin soja ba.

Sojoji ba su da wata jam’iyyar siyasa, ballatana ku yi tunanin za ku musu banbaɗanci kamar yadda kuke yi wa ‘yan siyasa. Babban ƙarfin ikonsu shi ne dakarun soji. A mafi yawan lokuta suna ƙwace iko ne ta hanyar juyin mulki. Wasu daga cikin juyin mulkin da suka yi sun kasance waɗanda aka zubar da jini, kamar dai na watan Janairu da Yulin 1966, a lokacin da aka kashe wasu fitattun shugabannin soji da na farar hula.

Sannan juyin mulkin da aka yi a watan Fabrairun 1976 shi ma ya kasance wanda aka zubar da jini, inda aka kashe Janar Murtala da wasu sauran manyan jami’ai, duk da cewa juyin mulkin bai yi nasara ba.

Sauran juyin mulkin kuwa ba a zubar da jini ba, waɗanda suka haɗa da wanda aka kifar da gwamnatin Gowon a watan Yulin 1975, da wanda aka kifar da gwamnatin jamhuriyya ta biyu a watan Disamban 1983, da wanda aka kifar da gwamnatin Buhari a watan Agustan 1985, da kuma wanda aka hamɓarar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Shonekan a watan Nuwamban 1993.

A ƙarƙashin mulkin Gowon da Murtala da Obasanjo da Buhari, Majalisar ƙolin Soji ta Supreme Military Council, SMC, ce babbar madafar iko a ƙasar, wacce take da ikon gudanar da aikin majalisa da na ɓangaren gudanarwa. A ƙarƙashin Babangida da Abacha da Abdulsalam kuwa, ana kiranta Majalisar ƙolin Soji da AFRC, amma dai kusan duk abu ɗaya ne. Sojojin na amfani ne da dokar sojoji mai matuqar ƙarfi; sai dai mu kunna rediyo kawai mu ji cewa shugaban ƙasa ya sanya hannu kan doka, wacce take da ƙarfin iko.

A ko yaushe idan aka samu sauyin gwamnatin soji, doka ta farko da sukan fitar ita ce wacce ake kira Constitution (Suspension and Modification) Decree, wacce take soke kundin tsarin mulkin ƙasa, wacce kuma ta dakatar da kundin tsarin mulkin dimokraɗiyya, ta soke majalisar dokoki da jam’iyyun siyasa, tare da miƙa dukan iko ga gwamnatin mulkin soja ta tarayya. Wasu daga cikin dokokin sojin masu tsauri ne.

Har yanzu mutane da dama na tunawa da Dokar Buhari ta Decree 4 ta 1984, wacce a ƙarƙashinta ne aka ɗaure ‘yan jarida kan wallafa labarin da yake na gaskiya ne. Sannan kuma akwai wata dokar soja mai tsauri ta ‘Miscellaneous Offences Decree’ mai lamba 18 ta shekarar 1985, wacce ake hukunta masu laifuka irin su satar amsar jarrabawa da lalata wayoyin kamfanin wutar lantarki NEPA, inda ake yanke musu hukuncin zaman gidan kaso mai tsauri ko ma hukuncin kisa. Wasu daga cikin tanade-tanaden dokar sun qunshi hukunce-hukunce soke ikon yin hukunci ko shari’a daga kotuna.

A lokacin da sojoji suke mulki, an saba ganin shugabanninsu cikin kakin soja da ya sha sitaci da guga, a maimakon gwamnoni da ministoci da shugabannin ƙasar farar hula da muke gani cikin tufafi na alfarma a yau. Sojojin na yawan tsare gira da muzurai da gajen haƙuri amma kuma suna aikinsu yadda ya kamata. Suna son a yi komai cikin gaggawa ba tare da vata lokaci ba.

Sukan kori ma’aikatan gwamnati kan laifi ƙanƙani, sannan wasu gwamnonin mulkin sojan kan zane ‘yan kwangila a bainar jama’a. Amma idan za a yi wa sojojin adalci, to su ne suka yi wa Nijeriya ayyuka da dama tun bayan samun ‘yancin kanta. An yi wa mafi yawan manyan tituna kwalta ne a zamanin mulkin soji. Mafi yawan gadoji da filayen jiragen sama da jami’oi da asibitocin ƙwararru da tashar jiragen ruwa da matatun man fetur da manyan masana’antu duk an gina su ne a qarqashin mulkin soja.

A yadda muka lalace a yau da karya doka da satar kuɗin gwamnati da satar amsar jarrabawa da zagin shuwagabanni da kwasar ganimar kayan gwamnati kuna ganin mulki soja irin na Buhari ko Abacha zai dace da mu?

Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya ya ƙare ƙasarmu Nijeriya daga mulkin soja, ya shiryi shuwagabaninmu, Amin.

Ɗalibi, Marubuci/manazarci, Mohammed Bala Garba, ya rubuto ne daga Maiduguri,
jihar Borno.